✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho ya sake kafa sabon tarihi

Mourinho ya kafa sabon tarihi bayan lashe gasar Europa Conference League.

Jose Mourinho ya kafa tarihi bayan kungiyarsa ta Roma ta yi nasarar lashe kofin Gasar Europa Conference, inda ya doke Feyenoord da ci daya da nema.

Wannan dai shi ne karo na biyar da kochin ya ci irin wannan kofi na gasar wasannin Turai a tsawon lokacin da ya dauka ya na horas da ’yan wasa.

Wannan nasara da Mourinho ya samu ta sa ya barke da hawaye saboda tsananin farin ciki, wanda ba ya rasa nasaba da sukar da yake sha daga masoya kwallon kafa cewa a yanzu ba ya tabuka komai a harkar horas da ’yan wasa a yanzu.

A halin yanzu dai Jose Mourinho shi ne mai horas da ’yan wasa na uku a duniya da ya ci manyan kofunan gasar wasannin Turai har sau biyar a cikin shekara 22, wato kamar yadda takwarorinsa Sir Alex (Ferguson) da Giovanni Trapattoni suka yi irin wannan, a lokacin da suke horas da ’yan wasa.

Kazalika a wannan lokaci dai Mourinho ya kasance na farko da ya kai wasannin karshe biyar tare da lashe dukansu a gasar Turai.

Ya samu wannan nasara ne a kungoyin da ya horas da ’yan wasa; FC Porto, Inter Milan, Manchester United da kuma Roma.

Wannan dai shi ne kofi na farko da  Mourinho ya ci wa Roma, tun bayan zuwansa a matsayin sabon mai horaswa.