✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MSSN na son gwamnati ta raba wa makarantun Legas hukuncin kotu kan sanya hijabi

MSSN na son makarantun jihar su fara aiki da dokar

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa (MSSN) reshen Jihar Legas sun yi kira ga gwamnatin Jihar da ta tabbatar da raba kwafin dokar tabbatar da sanya hijabi ga mata Musulmi a makarantun Jihar da Kotun Koli ta yi.

Shugaban kungiyar reshen Jihar, Malam Muftahudeen Thanni  ne ya bayyana hakan a taron manema labarai ranar Laraba a Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a ranar Juma’a ce dai Kotun Kolin Najeriya ta ba mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantun gwamnati da ke fadin Jihar ,

Da yake taya kafatanin musulmin Jihar murna, Thanni ya ce wannan hukuncin ya kara tabbatar musu da ‘yancinsu na yin shiga daidai da tsarin addinin Musulinci, bayan shafe shekara 10 suna fafatawa a kotu kan kudirin.

Ya ce, “Yanzu abin da ya rage wa gwamnati shi ne gurfanar da bata-garin da ke da kunnen kashi daga malaman makarantar Jihar idan sun ki bin wannan dokar.

“Sai kuma batun raba kwafin dokar ga dukkan makarantun da ke karkashin ikon gwamnatin Jihar wata guda bayan zartar da dokar.

“Akwai kuma bukatar gwamnatin ta yi wani zaman tattaunawa da MSSN ta jihar, da jagororin Musulmi da sauran kungiyoyin addinin Musulinci kan girman hijabin da hanyoyin amfani da shi ga matan,” inji shi.

A karshe ya yaba wa alakalan da suka zartar da wannan doka, domin dakatar da abin da ya kwatanta da cin zarafi da kuma take Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.