✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu da ma’aikatan gwamnati ba mai son a magance matsalar tsaro —Dan bindiga

Hirar waya da dan bindiga inda yake bayyana abubwan da ke faruwa.

Wannan wata tattaunawa ce ta murya da Aminiya ta samu a tsakanin wani dan bindiga da wani mai suna ciyaman da muke kyautata zaton ko dai ciyaman na Miyetti Allah ne a yankin Safana ko makwabtanta da ke Jihar Katsina ko kuma shugaban wani kwamitin sulhu na yanki.

A cikin tattaunawar dan bindigar ya yi zargin cewa su da ma’aikatan gwamnati da suke cin gajiyar ta’asar ’yan bindigar ba sa fata a kawo karshen wannan ta’addanci:

Dan bindiga: Kullum dabarar zalunci sai karuwa take. In ka tsaya ka natsu sai ka ga kullum karuwa ake da zalunci iri-iri.

Ciyaman: Kullum karuwa ake yi ana canja wa abin salo.

Dan bindiga: Yanzu ka duba ka gani kai Ciyaman, dajin nan Gabas daga Alhaji Ruga sai Ni da Bara, sai su Shafi’u, mu kawai ne

Ciyaman: Gaskiya ne

Dan bindiga: To yanzu idan ka kirga nan Gabas gangaren Gulbi, ni wallahi don na yi firi, amma wallahi kacalla-kacalla nan gangaren gulbi ran nan da na kirga daffo-daffo sai da na kirga goma sha hudu.

Ciyaman: Sha hudu?

Dan bindiga: ’Yan kayanka idan suka yiwo Yamma, daga a neme ni ko su Shafi’u. A ce wurina a ce wurin su Shafi’u. Kur’ani yanzu ka duba ka gani su rabin Jimna su rabin Tsaskiya akwai daffo shida.

Ciyaman: (Dariya) Kuma duk yaran ne kowa ya kama wuri nai.

Dan bindiga: Yo mu yanzu yara kanana sai dai lallashi. Yo mu yanzu da ka nemi ka matsa wa yaro zai ci mutuncinka. Yaro karami bai jin magana, ya baro gidan ubansa ya kama iskanci.

Ciyaman: (Dariya da shewa) Wallahi tallahi ko. Eh, na yarda.

Dan bindiga: Wallahi ni kam Ciyaman harkar nan da ta tawa ake yi da an dan dubi harkar nan an daga wa Habe dama sun samu sun yi noma. Ka duba ka gani, yara da rana sai su ruga su shiga garuruwa Ciyaman a bi gonaki. Wannan abu yana ta da mani hankali. Ni kowa na kallon abin nan, ni wallahi na so a sa masa ido. A ci da rana. A bi mutane gona-gona ana neman san huda ko mutum a dauke saboda Allah? Hari da sai da daddare, hari yanzu ya koma da rana Ciyaman ina lafiya?

Ciyaman: Babu lafiya. Wallahi ba lafiya, gaskiya ne.

Dan bindiga: Gaskiya abin, kuke tare da gwamnati ku dan ba ta shawara, ko da ita gwamnatin ba ta motsa ba, hukumar gargajiya don Allah ta dan motsa don a nemi maslaha ko yaya take, ko yaya take, a sama wa mutane a samu yadda aka yi.

Ciyaman: Gaskiya ne.

Dan bindiga: Tsakani da Allah wannan harka fa ta isa mu duba ta, hidimar nan fa ta fa wuce a yini. In kun lura kullum karfi take karawa. Duk wanda ya taso da abin da zai kama, duk wanda ya taso da abin da zai kama. Kowa in dai ya taso ba mai neman alheri.

Ciyaman: haka ne.

Dan bindiga: To wallahi wannan Gaskiya ne. Wallahi hidima Ciyaman ku ba da shawara, in an ki shawararku kuma shi ke nan mu taru mu zura ido.

Ciyaman: Shi ke nan kuwa.

Dan bindiga: To ai in aka kiya Ciyaman tunda kai kadai ba ka iya kawo zaman lafiya sai ka yi hakuri. Wallahi shekaranjiya abin da ya ba ni tsoro ka duba yadda wadansu yara da suka ribaba can kusan Kurfi wajen gidajen surukanmu wallahi Ciyaman komai da komai an tattaro ba inda na tare yaran nan Kur’ani na samu abin da na samu sai da na wuce Sha’iskawa. Wallahi rabon da in ketare titin nan tun bara da ka ji na ce zan yiwo wuni wajen walima gidajen, Kur’ani Ciyaman kufai ne. Yo ai daji, kai Ciyaman ya koma Gabas hauka kawai ake ta yi wallahi.

Ciyaman: Subhanalillahi.

Dan bindiga: Wallahi da ka kada daga nan in ka wuce Ummadau ka dauki babur dinka ka yi Gabas ba garin da kake tsoro, ba gida ba wani abin da kake tsoro sai ka kai wajen Sha’iskawa za ka ga gidaje kalilan dalilin su ma sai ka kai wani tsohon dan gari, da ka wuce su nan babu sauran wani gida sai ka kai Wurma wallahi, ina lafiya?

Ciyaman: Babu zaman lafiya ko kadan

Dan bindiga: Gaskiya Ciyaman ku ba da shawara. Ka ga ga mutanen Gora nan ina ta fama da su in shawo kansu. Ga mutanen Tsaskiya an hana su noma. Gaskiya Ciyaman wannan hidima duk ku duba ta. Su mutanen Gora korafi suke yi na kamun Abdul’azi ake yi, yara sun ki dadi. In ka hana wadannan yau, gobe sai ka ji sun aikata maka can ba ka sani ba.

Ciyaman: Gaskiya ne, gaskiya ne.

Dan bindiga: A dan kira mutane Ciyaman a dan yi shawara, ni dai kwanan nan kam na karyo, na kai mako biyu gaba dai shawara kawai nake jira, Kur’ani Ciyaman abin nan ya ishe ni. Tashin hankalin da nake duba wa mutane bai kirguwa Ciyaman. Abin mu dan duba shi ko ’yar balulluba a yi wa mutane masu gona.

Ciyaman: Haka ya kamata Sani, wallahi tuntuni nake ta wannan shawarar wallahi.

Dan bindiga: Damina dai ta taho, a samu ko sarakunan gargajiya a yi magana da su nan a samu ’yan dattijai a hada a yi magana da su don mu bi yaran nan su rage karfi. Kullum karfi suke karawa. Idan mutum ya je ya samo ’yan shanunsa uku ko hudu babu abin da zai hada sai kudin bindiga shin ina lafiya Ciyaman?

Ciyaman: Babu lafiya, wallahi babu ko kadan.

Dan bindiga: Ka lura Ciyaman yau idan aka yiwo kidinafin in dubu dari biyar aka karba, ciko ake nema a sayi bindiga ko bulet, shin ina lafiya Ciyaman?

Ciyaman: Babu

Dan bindiga: Yanzu ka duba bara da aka yi gyara, daga ni sai su Shafi’u Alhaji Ruga sai tsinta-tsinta. Amma ka duba yanzu in ka yiwo gabashin nan kafin ka kawo gidan su Malam Aibo, daffo-daffo abin da na lissafa ma da ke cikinsa gangariya wallahi daffo bakwai ke cikin shi. Babu inda za ka je ba ka iske bindiga goma ba. Kwata-kwata ba wurin.

Ciyaman: Subhanallahi!

Dan bindiga: Wannan abu ai ka ga ba lafiya. In ka lura da ka matsa nan wajen Umbadau za ka tarar da daffo tsakiyar karkara tsakiyar gonaki. Za ka tarar da bindiga goma, bakwai har zuwa uku. Kai harkar nan Ciyaman ni kam gaskiya na karaya. Ciyaman ku yi magana

Ciyaman: Insha Allahu Sani za a yi magana.

Dan bindiga: Gaskiya Ciyaman ni ko da shugabannin naku da kuke gani hada ni da wani in yi magana da shi. Gaskiya harkar nan a duba ta gaskiya ba ta da kyau. Ka duba Zamfara, da an yi tashin hankali sai a yi magana da manyan nan sai a rurrufa sai a gyara mutane su samu yadda suka fita suka nemi abinci, amma mu nan Katsina ba a yi an rike abu an yi shiru. Su ba su yaki mutane ba, su kuma ba su bari aka gyara ba aka samu inda aka tsugunna ba don Allah. Gara lokacin da ake kiran mu, wane ya koro mu tara mu amsa, a yi wannan a yi wannan. Wallahi gara sannan da yanzu.

Ciyaman: Gaskiya ne.

Dan bindiga: Gaskiya wannan Ciyaman ku dan duba mana ita mu samu sauki.

Ciyaman: Kana da lambar CP?

Dan bindiga: CP na ina?

Ciyaman: Na Katsina, Kwamishina.

Dan bindiga: Kwamishinan ’Yan sanda?

Ciyaman: Eh.

Dan bindiga: Ina da lambarsa. Amma ni ina ga CP kamar bai damu da hidimomin sauki ba, ko ko ya damu?

Ciyaman: A’ a. Da ka karanta masa wannan bayanin da ka yi mani, ai duk mai hankali da ya ji wannan bayanin ya san maganar hankali ce aka yi.

Dan bindiga: Eh, gaskiya ne.

Ciyaman: Eh, ka ga kowa ya gane wannan abu ka gaji da shi so kake a zauna lafiya

Dan bindiga: To wai kai fa Ciyaman wurin nan ina matsayin shugaba ne, amma wani abin ban iya hana shi, tunda in ba gani na yi da idona ba. Ina da karfin da zan hana kowa amma sai wanda na gani da idona.

Ciyaman: ne.

Dan bindiga: Amma in ban gani Gaskiya ne, gaskiya da idona ba, ban iya hanawa, sai dai inji an aikata, a kasha, a yi wannan, a yi wannan. Yanzu ga hidima nan ina so in gyara ta. Mutanen Taskiya na neme su gaba daya, mun fara maganar ran nan sai suka ce mani sai sun nemi Eriya Kwamanda sun tattauna. Wallahi Ciyaman in gaya maka, ma’aikacin gwamnati da barawo idan suna son zaman lafiya kada Allah Ya ba ni abin da zan ci, in dai ido za a sa musu bai tsayawa. Ai ka lura Ciyaman. Yanzu bari in maka dan karamin misali, lokacin da muke zuwa gidan gwamnati ana dan ba mu kudaden kashewa, mu da ku muna karuwa. Hidimar da ake mana mu da su don Allah muna so ta wuce?

Ciyaman: Ba a so (dariya).

Dan bindiga: Ka ga ba mu fa kaunar ta wuce, mu da su dukkanmu kowa na da kudi amma dan abin nan da ake ba mu, amma don Allah da aka raba mu ba mu dan matsu ba kafin mu dayaye?

Ciyaman: An matsu (dariya) gaskiya ne.

Dan bindiga: Yo wannan hidimar haka take in gaya ma. Da barawo da mai tafiya ya tarar da mutum ya amshe kaya da ma’aikacin gwamnati wanda za a ce masa ga barayi can ya fita, in su za a biye wa in abin nan ya wuce kada Allah Ya ba ni abin da nake nema. Wallahi bai wucewa kwata-kwata. Yo ai sana’a ce. Kowa bisa sana’arsa yake. Yanzu ka lura kai Ciyaman, in an fashe gaba daya kowa abin da zai ci yake nema bai lura da abin da ke cin sa.

Ciyaman: (Dariya) Gaskiya ne.

Dan bindiga: Ni dai ina so abin nan in so samu ne cikin mako biyu a duba.

Ciyaman: Ya yi nisa Sani. Yau din nan ma zan je Katsina. Wannan maganar taka ai ta tsima ni.

Dan bindiga: Ka san abin nan Ciyaman in ba a tsai da shi ba? Wallahi in badi warhaka in aka ce Safana ta yi kwai kada ka yi gardama na rantse da izihi sittin na Kur’ani. Ka duba duwatsun nan na Arewacin Safana duk an kore mutanen da ke nan kaf duk an kore su ba su noma nan. Mafi yawa matsawa suke za su shige duwatsun nan yaya ka ga za a yi?

Ciyaman: Kur’ani an samu matsala.

Dan bindiga: Ku duba mana abin nan bai da kyau kwata-kwata. In ka je yi mani filashin kowane ne ka samu, ko shugaba ne Kur’ani ina iya magana da shi in gaya masa gaskiya. Ban ce a gyara duka ba, tilas a yi wa barawo yadda yake so, amma don Allah a sa sarakunan gargajiya su yi magana da su a samu a gyaggyara ’yan kasuwannin da ake kaiwa ko’ina a dudduba, a kyale yara can su tafi su yi harkarsu. ’Yan harkokin nan a samu sauki manoma su samu sauki. Harkar nan Ciyaman ba ta da kyau tsakani da Allah.

Ciyaman: Gaskiya ne. To babu matsala Sani in na je Katsina zan sanar. Na gode, ka yi tunani mai kyau.

Dan bindiga: Ni ma na gode.