✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu guji siyasar kwadayi da kabilanci a 2023 —Bin Uthman

Sheikh Bin Uthman ya ce a guji zaben SAK

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Bin Uthman Kano ya bayyana siyasar kwadayi da kabilanci a matsayin daya daga cikin dalilai da ke jawo koma baya a cigaban kasa.

Malamin wanda ya bayyana haka a yayin laccar da ya gabatar a Masallallacin Juma’a na Annur da ke Abuja mai taken “Saba-ta juya-ta…Ina mafita a siyasar Najeriya,” ya kuma buqaci al’umma da su guji siyasar SAK.

“Ku mayar da hankali wajen zabar cancanta da zaban shugabanni na gari wadanda za su kare muku muradunku, ba tare da la’akari da banbance-banbance ba,” inji Sheikh Bin Uthman.

Ya ce siyasa ta zama wata sila a sabuwar dokar duniya, da kusan ya zama hanya daya tilo da dole kowa ya yi ta, “Idan kuma kun ce ba za ku yi ba, to za a bar ku a baya.”

Sheikh Bin Uthman wanda shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kundila da ke Kano, ya ce gudummawar da za a iya bayar wa a siyasa a daidaiku, zai samu nasara ne kawai ta hanyar katin zabe.

Daga nan ya buqaci jama’a da su mallaki katin zabe.

Laccar ta gudana ne daga karfe 7 na zuwa 9 na dare ranar Juma’a.