✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu leka Indiya: Fina-finan da suka fi kawo kudi a 2020

Masana’antar shirya fina-finai ta Kasar Indiya Bollywood ta fitar da jerin wasu fina-finai da suka samu gagarumar riba a shekarar da muke bankwana da ita.…

Masana’antar shirya fina-finai ta Kasar Indiya Bollywood ta fitar da jerin wasu fina-finai da suka samu gagarumar riba a shekarar da muke bankwana da ita.

Duk da yadda cutar coronavirus ta targada tattalin arzikin duniya, wanda ya shafi kowane bangare na rayuwa ciki har da masana’antar ta Bollywood.

Ga jerin fina-finan da suka ci riba:

  1. Fim din ‘Tanhaji’ wanda kamfanin Ajay Devgn FFilms T-Series ya shirya shi kuma kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dalar Amurka miliyan 52.
  2. Fim din ‘Baaghi 3’ wanda kamfanin Nadiadwala Grandson Entertainment Fox Star Studios ya shirya shi kamfanin Fox Star Studios ya yi dillancinsa ya samu Dala miliyan 19.
  3. Street Dancer 3D’ wanda kamfanin T-Series Remo D’Souza Entertainment ya shirya shi kuma kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan14.
  4. Shubh Mangal Zyada Saavdhan’ wanda kamfanin T-Series Colour Yellow Productions ya shirya shi kuma kamfain AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan.
  5. Malang’ wanda kamfanin T-Series Luv Films Northern Lights Entertainment ya shirya shi kamfanin Yash Raj Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 12.
  6. Fim din ‘Chhapaak wanda kamfanin Fox Star Studios Productions Mriga Films ya shirya, Fox Star Studios ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 7.8.
  7. Love Aaj Kal’ wanda kamfanin Maddock Films Window Seat Films Jio Studios Reliance Entertainment ya shirya shi, kamfanin Pen Marudhar Entertainment ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 7.4.
  8. Jawaani Jaaneman’ kamfanin Pooja Entertainment Black Knight Films Northern Lights Films ya shirya shi, kamfanin Pen Marudhar Entertainment ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 6.3.
  9. Thappad’ wanda kamfanin T-Series Benaras Media Works ya shirya shi, kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu Dala miliyan 6.2.
  10. Fim din ‘Panga’ wanda kamfanin Fox Star Studios ya shirya shi, kuma ya yi dillancin kayansa, ya samu Dala miliyan 5.8.