✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu lizimci kididdiga da hisabi a rayuwa (2)

Ma’abuta shan gurbiyar Sinadarin Rayuwa, ga sallamar da muka saba yi wa juna, Assalamu alaikum. Bayan haka, a makon jiya muka faro wannan maudu’in, da…

Ma’abuta shan gurbiyar Sinadarin Rayuwa, ga sallamar da muka saba yi wa juna, Assalamu alaikum. Bayan haka, a makon jiya muka faro wannan maudu’in, da ke yi mana jagora ga rayuwarmu ta yau da kullum. Wannan kuwa shi ne, yadda za mu gane muhimmancin kididdiga da hisabi a rayuwarmu ta yau da kullum, ga ci gaba:

Ya dace mu gane cewa, Allah cikin ikonSa da hikimarSa, Yana gudanar da al’amura ne bisa kididdiga da lissafi. Yana saukar da komai bisa iyakantaccen adadi da awo bisa mizani irin naSa. Dalili ke nan idan muka lura da al’ummar duniya da suka ci gaba wajen kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, su ma da kididdiga da mizani suke amfani. Mu duba mota da jirgin sama da sauran abubuwan rayuwa da suka kera, za mu ga cewa komai na jikinsu a kidaye yake. Me zai hana mu ma mu kasance cikin wannan halayayya? Lallai kam za mu girbi dinbin alheri idan muka lizimci amfani da kididdiga.

Kamar yadda muka ambata da farko, bayan kididdiga, hisabi ma abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Kamar yadda muke da yakinin cewa ranar lahira za mu fuskanci awo da hisabi, to kamata ya yi tun a nan duniya mu rika yi wa kanmu hisabi a kullum.

Abin da ya kamata mu rika yi shi ne, a kullum da dare, bayan mun kwanta a shimfidarmu, kafin mu kai ga yin barci, sai mu yi tariyar dukan abubuwan da muka aikata a wannan rana. Mu gano abubuwan da muka yi na alheri da kuma wadanda muka yi na sharri, da wadanda muka yi bisa kuskure ko mantuwa. Idan muka kididdige wadannan ayyuka, sai mu ba kowane aiki irin darajarsa, ta nasara ko kuma ta faduwa. Idan nasara ta rinjayi faduwa, mun ci nasara ke nan a wannan rana. Idan kuwa muka samu faduwa ta rinjayi nasara, ke nan sai mu yi wa kanmu ladabin da ya dace ke nan.

Idan muka yi haka, gobe idan mun farka, za mu yi wa kanmu fada, sannan mu shirya yadda za mu tunkari wannan sabuwar rana. Idan jiya mun samu makin nasara mai yawa, sai mu yi azamar ninka irinsa. Idan kuma mun samu makin faduwa mai yawa, sai mu shirya yadda za mu kauce wa sake aikata shi. Lallai kam wannan shi ne tsari mai kyau da ya kamata mu sanya cikin rayuwarmu. Ta haka za mu rika yin rayuwar da ta dace da mu, a matsayinmu na mutane ’ya’yan Adamu, wadanda aka ba hankali da basira. Ke nan za mu bambanta da dabbobi, wadanda ke rayuwar kara-zube.

Allah Ya sanya mu dace, amin. Sai kuma mako na gaba, idan Allah Ya kai mu!