Mu ne muka kai hari kurkukun Kuje —ISWAP | Aminiya

Mu ne muka kai hari kurkukun Kuje —ISWAP

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram
    Sani Ibrahim Paki

Kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP ta ce mayakanta ne suka kai hari a kan gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, a daren Talata inda aka saki daruruwan fursunoni.

Aminiya ta rawaito yadda maharan suka saki fursunoni sama da 800 yayin harin, ciki har da rikakkun mayakan Boko Haram da ISWAP.

A cikin wani sabon bidiyo da ta fitar da maraicen Laraba, ISWAP ta kuma nuna yadda wasu daga cikin mayakanta suka rika harbi har suka shiga cikin gidan.

A cikin bidiyon, an ji mayakan suna kabba suna cewa, “Daukar Musulunci ba za ta gushe ba.”

Wani sako da ISIS ta fitar a shafinta a rabar Laraba da dare ya ce, “Mayakan Daular Musulunci (IS) sun kai hari ranar Talata da dare a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, inda suka rusa katangarsa suka kuma kubutar da gomman futsunoni.”

Muna tafe da karin bayani…