✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Babu shaida

Wani Bahadejen dan sanda ne ya kama wani a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku. Ga yadda ta…

Wani Bahadejen dan sanda ne ya kama wani a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku.

Ga yadda ta kwashe a tsakaninsu:

Mashayi: “Ba ni da laifi, a kullum na zo dakin bahayar nan, idan na nemi kore su sai kawai in ga sun fada aljihuna. Abin kamar na jinnu.”

Bahadeje: “Ka dauke ni wawa ne, kana son in amince da wannan karyar?”

Mashayi: “Bari in tabbatar maka da gaskiyata.”

Bahadeje ya mika wa Mai Laifi wiwin da ya kwace daga wurinsa, ya ce masa: “To tabbatar mani, in gani.”

Koda ya amsa sai ya zuba su a tukunyar kora kashi, ya danna ruwa suka bace.

Ganin haka sai Bahadeje dan sanda ya ce: “To, nuna mani aljihunka in ga yadda wiwi ta koma.

Shi kuwa mai laifi ya ce: “Wace wiwi kuma?”

Daga nan ne sai dan sandan ya fahimta ashe wayau ya yi masa.

Ga shi yanzu bai da damar kama shi, tun da babu shaida.

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011