✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Bakano a Banki

Na zaci shi ne netwok, da na ci masa mutunci.

Wani Bakano ne mai gadin makarantar firamare, da karshen wata ya yi sai aka tura masa albashinsa ta banki.

Da ya je bankin don cire kudin, ya mika takardar cire kudi sai mai biyan kudin ya ce da shi: “Ba netwok.”

Sai ya sami wuri ya zauna. Ya zauna na tsawon awa uku, can sai ga wani ma’aikacin bankin ya shigo ya zauna, jama’a na zuwa wurinsa don bukatunsu.

Ai Bakanon nan sai ya mike ya nufi wani mai gadin bankin ya tambaye shi cewa: “Wancan mutumin ne network din da ake jira? Sai ya amsa da cewa ba shi ba ne.

Bakano ya ce: “Na zaci shi ne netwok, da na ci masa mutunci.”

Daga Ibrahim A. B. Balarabe Zariya City