✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Dan damfara

Mutumin ya ce komai wuya zai bi sharadin.

Wani mutum ne yake son ya zama mai kudi a kankanin lokaci, sai ya je wajen wani boka ya taimaka masa.

Sai kuwa ya ce zai taimaka masa ya zama mai kudi amma sharadin abin akwai wuya.

Shi kuwa ya ce komai wuya zai bi sharadin.

Ya ce masa ya kawo Naira dubu dari, za a hada masa magani.

Da ya kawo kudin, nan take boka ya yi wata hikima, ya boye su, ya fito da na bogi ya mika wa mutumin, ya ce masa: “Duk abin da na fada ka fada.”

Ya ce masa: “Daga kudin sama!”

Ya daga. Ya ce masa: “Ka ce sai an kona kudi ake neman kudi sau uku.”

Sannan ya ba shi ashana ya ce ya kunna wa kudin wuta.

Ya kuwa kunna musu wuta suka kone. Ya ce masa ya kwashe tokar, bayan ya kwashe, sai boka ya hada da wani garin magani.

Ya kwaba shi, ya ba mutumin, ya ce masa: “Idan ka je gida, ka yi wanka ka shafe jikinka da maganin amma sharadi shi ne, koda ka ji kaikayi, kada ka sosa.

“Idan kuwa ka sosa, to maganin zai karye.”

Ya yi wa boka godiya, ya tambayi ko nawa zai biya? Boka ya ce sai aiki ya yi kyau zai zo ya biya.

Mutumin ya tafi gida ya yi abin da boka ya gaya masa.

Ashe cikin magani akwai karara, kaikayi ya matsa masa, kamar ya daure amma ya kasa.

Nan ya tashi ya yi ta susa ba kama hannun yaro.

Daga Muhammad Shamawilu Shafi’u Kofa