✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muharram: A soma duban wata ranar Lahadi — Sarkin Musulmi

A soma duba jinjirin watan Muharram daga yau Lahadi.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su soma duban watan Muharram daga ranar Lahadi 29 ga watan Zhul Hijja Bayan Hijira wanda ya yi daidai da 8 ga Agustan 2021. 

Kwamitin bai wa majalisar sarkin Musulmi shawara kan har kokarin addinin musulunci karkashin Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid suka fitar da sanarwa a madadin Sarkin.

Sanarwar ta kuma nemi duk wanda ya ga jinjirin watan da ya kai labarin ga basaraken da ke kusa da shi domin sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko Kwamitin Ganin Watan na Kasa da masarauta.

Tuni dai wasu jihohin musulmi suka ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar musulunci don fadakar da al’umma kan muhimmancin shigowar sabuwar shekarar musulunci da kuma gudanar da addu’o’i.

A Sakkwato, wasu kungiyoyin addinin musulunci sun yi hadaka da Gwamnatin Jihar da Majalisar Sarkin Musulmi inda suka samar da Kalandar musuluncin da za a kaddamar a ranar Litinin ko Talata.