✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa a rikicin Tigray na kasar Habasha

Fira Minista Abiy Ahmed ya kirayi fararen hula da su shiga aikin soji su taimaka wa sojojin gwamanti.

Kusan wata 14 ke nan da yankin Tigray da ke Arewacin kasar Habasha ya fada cikin rikici, inda Fira Minista Abiy Ahmed ya tura dakarun gwamnati su tarwatsa ’yan tawayen TPLF da ke yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bincike kan zargin “matsanancin cin zali” a rikicin, duk da cewa gwamnatin kasar na adawa da hakan.

Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru a rikicin:

– 2020: Sojoji sun shiga Tigray

Ranar 4 ga watan Nuwamban 2020 kasar ta fara daukar matakin soja bayan abin da Fira Minista Abiy Ahmed ya kira harin ‘cin amana’ da aka kai wa sansanonin sojin gwamnati a Tigray.

Ya zargi jam’iyyar TPLF mai mulki a yankin a hannu a harin. TPLF ita ce jam’iyyar da ta makaye siyasar kasar na tsawon shekara 30 kafin ya hau mulki a 2018.

– ‘Laifukan yaki’

Bayan kwana 10 ana yaki a Tigray, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin aikata laifukan yankin.

Kasar Iritriya mai makwabtaka da Habasa ta tura dakarunta domin taimaka wa sojojin gwmnatin Habasha a Tigray.

Idan ba a manta ba a 2018 Abiy ya shiga tsakani a rikicin Iritriya har ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya, wanda ya kai shi ga samun kyautar Nobel Kan Zaman Lafiya.

Bayan mako biyu dakarun gwamnati suka kwace Mekele, hedikwatar Tigray.

A ranar 28 ga Nuwamba, 2021, Fira Ministan ya sanar cewa “an kammala aikin,” amma duk da haka aka ci gaba da fada.

– 2021: ‘Kisan kabilanci’

A watan Fabrairun 2021 kungiyar ta zargi sojojin Eritriya da kashe “daruruwan fararen hula” a watan Nuwamba a birnin Axum.

A tsawon watannin, gwamnatocin Habasha da Eritriya sun musanta hannun dakarun Eritriya da kisan kabilanci, zargin da gwamnatin Amurka ke musu.

Amma a ranar 23 ga watan Maris, Abiy ya amsa cewa dakarun Eritriya sun shiga kasarsa, jami’an gwamnatinsa kuma sun ce sojojin sun kashe sama da fararen hula 100 a Axum.

An gudanar da zabe a fadin kasar Habasha, amma hakan bai yiwu ba a Tigray.

– Dawowar mayakan Tigray

A karshen watan Yuni ’yan tawayen Tigray suka sake dawowa suka kwace Mekele, daga nan suka nausa suka kwace yankunan Amhara da Afar da ke makwabtaka.

A watan Yuli Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 400,000 na gab da fadawa cikin matsanancin yunwa a Tigray.

’Yan tawayen sun yi watsi da kiran da gwamnatin Amurka da yi musu na janyewa.

A ranar 10 ga watan Agusta, Fira Minista Abiy Ahmed ya kirayi fararen hula da su shiga aikin soji su taimaka wa sojojin gwamanti.

– Kawancen ’yan tawaye

Ranar 4 ga watan Oktoba Abiy ya karbi rantsuwar fara aiki a wa’adin mulkinsa na biyu na tsawon shekara biyar.

Bayan mako biyu jiragen sojin kasar suka kaddamar da hare-hare a Mekele da wasu wurare a Tigray.

A tsakiyar watan Oktoba, ’yan tawayen suka yi ikirarin kwace muhimman wurare biyu a birnin Amhara — mai tazarar da kilomita 400 daga Arewacin Addis Ababa, babban birnin kasar.

Gwamnati ta yi watsi da ikirarin sannan a ranar 2 ga watan Nuwamba ta sanya dokar ta-baci a fadin kasar.

Washegari wani rahoton hadin gwiwar gwamnatin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai yiwuwar aika laifukan tauye hakkin dan Adam daga bangarorin da ke yakin.

– Kiran tsagaita wuta

Kasashe da dama, ciki har da Amurka, sun bukaci ’yan kasarsu su fice daga Habasha.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a tsagaita wuta.

Ranar 12 ga Nuwamba, Amurka ta sanya takunkumi ga jam’iyya mai mulki da sojojin Habasha.

– Fira Minista a filin daga

Ranar 24 ga watan Nuwamba 2021 Abiy da kansa ya hallara a filin yaki, ya jagoaranci hare-hare kan ’yan tawaye.

Bayan kafafen yada labaran gwamnati sun fitar da rahoton, washegari gwamnati ta sanya sabbin iyakoki kan fitar da bayanan yakin.

Ranar 1 ga Disamba, gwamnatin ta sanar da kama garuruwa da dama, cikin har da Lalibela, daya daga cikin wuraren tarihin Majalisar Dinkin Duniya.

Jiragen kayan agajin Majalisar Dinin Duniya sun ci gaba da kai-komo tsakanin birnin Addis Ababa da Mekele.

Bayan kwana biyar, gwamnatin kasar ta yi ikirarin kwace muhimman garuruwan Dessie da Kombolcha.

Abiy ya sanar da komawarsa Addis Ababa bayan mako biyu a filin yaki.

Bayan nana ’yan suka sake kwace Lalibela a ranar 12 ga Disamba.

– Binciken MDD kan cin zarafi –

Ranar Juma’a Hukumar Kare Hakki ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bincike kan zargin cin zarafi a yayin da ake fargabar karuwar tauye hakkkin dan Adam a rikicin.

Gwamnatin Habasha dai ta fito kai da fata wajen nuna rashin amincewarta ta binciken, wanda ta kira “sabon salon mulkin mallaka”.