✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubuwan da Buhari ya tabo a jawabinsa na sabuwar shekara

Ya fara da godiya marar iyaka ga Mai Duka da ya azurta mu da ganin wata sabuwar shekarar.

A yayin da a yau Asabar muka shiga sabuwar shekara wadda ta yi daidai da 1 ga watan Janairun 2022, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da sakon taya murna ga ’yan Najeriya.

Shugaba Buhari ya fara da godiya marar iyaka ga Mai Duka da ya azurta mu da ganin wata sabuwar shekarar a matsayin kasa daya dunkulalliya, duk da irin kalubalen da ake fuskanta masu yi wa ci gaban kasar zangon kasa.

Daga nan kuma Shugaba Buhari ya jinjina wa daukacin al’ummar kasar bisa juriya da suka nuna a shekarar da ta gabata ta 2021, sakamakon kalubalen da kasar ta fuskanta kamar sauran kasashen duniya na annobar Coronavirus a daidai lokacin da kuma ake kokarin farfado da tattalin arziki da samar da zaman lafiya.

Shugaban ya bayyana karfin gwiwarsa kan ci gaban da ake samu wajen inganta harkokin tsaro duk da irin koma bayan da ake samu, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zage damtse a kan tsare-tsarenta domin cika alkawuran da ta dauka na inganta rayuwar ’yan Najeriya.

A yayin da yake tunatar da yan Najeriya cewa babu wata kasa da ta fuskanci kalubale kuma a karshe ya zama tarihi a sakamakon jajircewarta da kuma tsayin da ta yi wajen shawo matsalolinta, Buhari ya kuma ce gwamnatinsa za ta sauya takun da take yi ta hanyar nemo wasu hanyoyin da suka hada da sasanci da sulhu domin kawo karshen matsalolilin da ake fuskanta kama daga na barayin daji da kuma ’yan Boko Haram a arewacin kasar, da kuma rikicin kungiyar IPOB a kudu maso gabashin kasar.

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta rubanya kwanzonta a kan harkokin tsaro wanda shi ta fi ba muhimmanci, inda ya ce za a inganta dukkanin hukumomin tsaro musamman na dakarun soji da yan sanda ta hanyar wadata su da kayayyaki yaki da makamaki na zamani domin tunkarar masu tayar da zaune da sauran kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya tuna sannan ya kuma yaba wa jarumtar jami’an tsaron da suka rasa rayukansu wajen tsare mutuncin kasar daga masu yi wa kasancewarta zagon kasa. Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafada-da-kafada da abokan hulda na ketare da kuma kasashen da ke makwabtaka da ita wajen shawo kan duk wasu matsalolin tsaro da za su bijiro domin murkushe tushensu tun kafin su samu gindin zama.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya yi waiwaye tare jajanta wa duk wadanda suka rasa ’yan uwansu a sakamakon matsalar tsaro, yana mai cewa rayuwa kowane dan Najeriya tana da matukar muhimmanci, lamarin da ya ce duk wani rashi da aka yi a kasar sakamakon matsalar tsaro ta shafe shi a matsayinsa na dan kasa kuma shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta gushe ba a kan dagewa domin ganin an kiyaye duk wasu tanade-tanade da kundin tsarin mulkin kasar ya yi ta hanyar tsare mutuncin dukkanin ’yan kasar daga kowane irin nau’i na cin zarafi a ciki da wajen kasar.

A bangaren tattalin arziki, jawabin shugaban na Najeriya ya tabo abin da ya kira, “juriyar da tattalin arzikinmu ya nuna duk da koma bayan da annobar Coronavirus wadda ta dabaibaye dukkan kokarin da kasashen duniya ke yi na gina kasa.”

Buhari ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da fiye da kashi 4 cikin 100  a rubu’i na uku na shekerar 2021 kamar yadda alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS suka bayyana, lamarin da ya ce hakan manuniyace a kan hobbasan da gwamnatinsa take yi ta hanyar shimfida tsare-tsare da manufofin da za su farfado da tattalin arzikin kasar.

Kazalika, ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu karuwar kashi 5 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2020 wanda ya ce ya fi na dukkan kasashen Afrika da ke Kudu da hamadar sahara, kuma ya zarce na dukkan shekarun baya-bayan nan musamman tun daga shekarar 2014.

Ya kuma tabo batun sanya hannun da ya yi a ranar 16 ga watan Agustan 2021 a kan Dokar Man Fetur ta Petroleum Industry Act mai zummar gyara lamurran hakowa da sarrafa albarkatun man fetur a kasar, inda ya yi godiya ta musamman ga Majalisun Tarayyar Kasar saboda hadin kan da suka ba gwamnatinsa wajen samar da wannan dokar da ya ce an shafe kusan shekaru ashirin ana kokarin samar da ita.

Shugaba Buhari ya sanar da ’yan Najeriya cewa daga wannan shekarar ta 2022, gwamnatinsa za ta rika rungumar fasahar sadarwa ta zamani a karkashin shirinta na samar da ayyukan yi ga ’yan kasar da bunkasa tattalin arziki, wanda ya ce dalilin haka ya sanya ’yan kasuwa na duniya ke tururuwar sanya hannun jari domin samun riba mai tsoka.

Dangane da cin da rashawa da ya bayyana a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da kasar nan take fuskanta, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta ci gaba da bai wa yaki da cin hanci da rashawa muhimmanci da hakan ne kadai zai daga darajar kasar da martabarta.

Shugaban kasar ya ce a yayin da ake maraba da sabuwar shekarar, ya nemi kowane dan kasar da ya yi wa Najeriya fata na gari da hasashen kyakkyawar makoma wadda za a kawo karshen duk wasu kalubale da take fuskanta na zamantakewar al’umma.