✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin kamshi a rayuwar mace

Mata su mayar da amfani da turare kamar yadda dole suke yin wanke-wanke.

Kamshi abin so ne ga kowa. Don haka, ya kamata mata su kasance masu yawan amfani da turare iri-iri kama daga na wuta da sauransu.

Ya kamata mata su mayar da amfani da turare kamar yadda dole suke yin wanke-wanke.

Ko kun san cewa za a iya amfani da turaren wuta da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa?

Bayan haka, akwai turaren humrah wanda za a iya shafawa a gashin kai.

Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga.

Tabbas duk macen da ta kasance cikin kamshi, za ta samu daraja da kima a wajen maigisdanta da sauran al’umma.

Haka kuma, akwai turaren kanti kamar su ‘Dior’ da cool water da sauransu.

Yadda za ai amfani da turaren gargajiya

A samu kabbasa (za a iya samun sa a Borno) da kasko, a zuba garwashin wuta, sannan a dora kabbasar a kai.

Sai a zuba turaren wuta a cikin garwashin, sai a dora kayan da ake son kamsasawa, ta yadda yakin zai shige su sosai.

Bayan an yi wanka, sai a shafa kulaccam (kamar man shafawa yake amma da turaruka ake hada shi) a matsayin man shafawa.

Sannan sai a sa riga, a shafa humra fara ko baka a jikin kayan. Idan kayan mai duhu ne, sai a shafa humra baka. Idan kuwa kayan masu haske ne, sai a yi amfani da farar humra.

Idan kuwa ana son amfani da turaren kanti, sai a fesa shi kawai.

Amma fa a sanai cewa, na gargajiya ya fi dadewa a jiki. Saboda ko kaya sun yi datti da kyar a ji warin dattin saboda kamshin turaren.

Haka kuma, irin wadannan turarruka na taimaka wa masu jego wajen rage karnin nono da kuma na jikin jariri. Wasu matan da zarar sun haihu, sai a ji suna karni.

Don haka, sai a kula wajen amfani da turare domin magance wadannan matsalolin.