✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin kyautata wa marayu

Limamin Masallacin ‘Yan Kaji da ke Alaba Rago a Jihar Legas ya jadadda mahimmancin taimaka wa marayu da matalauta a lokutan Sallah da sauran lokuta.…

Limamin Masallacin ‘Yan Kaji da ke Alaba Rago a Jihar Legas ya jadadda mahimmancin taimaka wa marayu da matalauta a lokutan Sallah da sauran lokuta.

Malamin ya ce yin hakan na da tasiri a rayuwar wadanda aka taimaka wa da mai taimakawan.

Shaikh Ahmad ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci raba wa marayu da marasa karfi naman Sallar Layya a masallacinsa.

Ya ce a karo na biyu ke nan suna yi wa marayu da marasa karfi a yankin layya domin su samu abun da za su ci su yi farin ciki kamar kowa.

“Yaron da ke da uba idan uban ba shi da halin layya yakan kasance cikin wani yanayi, …ina ga wanda ba shi da mai yi masa?

“Wannan shi ne dalilin da ya zaburar da mu domin debe wa marayu kewa tare da kyautata wa marasa karfi.

“Kuma alhamdulillahi mun bai wa akalla mutum 70, domin a bana bijimin sa muka saya na N300 muka yanka musu.

“Tabbas wannan abu ya yi tasiri a rayuwarsu da ma ta wadanda suka ba da taimakon”, inji shi.

Malamin wanda ya ce wasu bayin Allah ne a ciki da wajen kasar nan suka ba da taimako aka yi wa marayun layya, ya yi kira ga sauran masallatai da su yi koyi.

“Yawancin taimakon daga nesa ne muka tattaro don haka ina kwadaitar da mutanenmu na kusa a Alaba Rago su shigo a yi  wannan aikin lada da su.

“Akwai masallatai da dama, duk wanda yake da ikon tallafawa kada ya yi sake a bar shi a baya”, inji shi.

Aminiya ta zanta da wani mutum mai suna Malam Abdullahi Muhammad da ke rikon marayu biyar da suma suka amfana.

Ya bayyana murnarsa cewa ya samu damar yin bikin Sallah cikin walwala tare da marayun.

“Wannan tsari da Malam Ahmad Saleh ya kawo lamari ne na taimakon marasa galihu, muna fatan Allah Ya saka masa da duk wadanda suka ba da gudunmuwa”, inji shi.

Sallah Babba da ta gabata ta zo wa al’umma a lokaci na annoba lamarin da ya sa malamai suka yi ta jan hankalin jama’a su dage wajen tallafa wa marasa galihu domin samun rabo a gobe kiyama.