✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin shan madara ga lafiyar dan Adam

Madarar yogot na dauke da sinadaran calcium da bitamin B12 da sauransu.

Kwararriya a fannin kiwon lafiya, Dokta Bisi Abiola ta bayyana cewa, abu ne mai muhimmanci ga mutum ya rika shan madara a-kai-a-kai, wanda hakan na taimakawa wajen inganta lafiyar jiki.

Ta ce, madarar yogot na dauke da sinadaran calcium da bitamin B12 da sauransu, wadanda ta ce suna taimakawa sosai wajen gina jiki, domin kuwa sun kasance wasu bangarori na ingantaccen abinci.

Haka kuma ta jaddada cewa, madara na da muhimmanci wajen tsaftace jiki daga illar da ke haddasa taruwar kitse a jiki, kamar kuma yadda take karfafa kasusuwan jiki tare da inganta shakar iska mai lafiya da kuma saukaka tace abinci a jiki.

“Madarar yogot tana samar da kusan dukkan sinadaran da jiki ke bukata.

“Tana kunshe da sinadarai na musamman da suke taimakawa wajen rage kiba kuma tana sanya mutum ya samu dandano wajen cin abinci,” inji ta.

A cewarta, mutane su daina daukar madarar yogot a matsayin wani abinci mai dadi kawai, domin kuwa amfaninsa ga jikin dan Adam ya wuce batun dandano kawai.

Ta kafa misali da madarar Hollandia, wacce ta ce ta gamsu da yadda ake sarrafa ta, musamman yadda take dauke da dukkan sinadaran da ake bukata a madara, domin gina jiki da samar da ingantattar lafiya ga dan Adam.

A yayin da take kara misali, ta ce tun daga lokacin da aka fara sarrafa ta a Najeriya, an ci gaba da samar da madarar cikin inganci, ba tare da an rage mata wani bangare ba.

Wannan dalili ne ma ya sa aka fi raja’a a kanta kuma masana kiwon lafiya da kimiyyar abinci suka fi kafa misali da ita a kowane lokaci.