✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mukabalar Kano: Za a gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu

Tuni dai ’yan sanda suka gayyace shi ya bayyana ranar Litinin.

Mukabalar da aka jima ana sauraro tsakanin malamin nan na Kano, Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman Jihar ta gudana ranar Asabar ba tare da kowane bangare ya yarda da matsayin abokin fafatawarsa ba.

Sai dai bayan kammala mukabalar, Aminiya ta gano cewa ana shirye-shiryen gurfanar da Sheik Abduljabbar a gaban kotu bisa zargin aikata sabo, yunkurin tayar da zaune tsaye da sauran laifuka.

Tuni dai ’yan sanda suka mika masa goron gayyatar neman ya bayyana a shalkwatar ’yan sandan Jihar ranar Litinin.

Wata majiya da ke da kusanci da malamin ta shaida wa wakilanmu cewa an shirya tuhumce-tuhumcen da za a yi masa ne daga wurin mukabalar da aka yi a Hukumar Shari’a.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da gayyatar a ranar Asabar, ko da yake ya tsaya kai da fata cewa gayyatar bata da alaka da mukabalar da aka yi.

“Yana daya daga cikin tuhumar da ake masa wacce yanzu haka dama a karkashin beli yake. Akwai tuhumar da wasu malamai suke masa, kuma ya jima yana zuwa shalkwatar ’yan sanda a bangaren binciken.

“Tun ranar Juma’a ya kamata ya zo, amma saboda shirye-shiryen mukabalar, sai muka dage don a bashi damar shirya mata yadda ya kamata,” inji Kiyawa.

Malaman da suka fafata da Sheik Abduljabbar a mukabalar dai sun hada da Dokta Rabiu Umar Rijiyar Lemo da Malam Mas’ud Hotoro da Malam Abubakar Mai Madatai da kuma Malam Kabir Bashir Kofar Wambai.

Daga karshe dai alkalin mukabalar, Farfesa Salisu Shehu ya ce malamin ya gaza amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa inda ya rika yin kame-kame.

To sai dai malamin ya yi zargin cewa ba a bashi cikakken lokaci domin ya kare kansa ba, inda ya roki gwamnati ta sake shirya wata mukabalar a nan gaba.