✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mummunan mataki zai biyo baya idan Rasha ta mamaye Ukraine – Kungiyar G7

Kasashen sun ce matukar ta mamaye Ukraine, za su hukuntata.

Kungiyar Kasashe Mafiya Girman Tattalin Arziki a Duniya ta G7 ta yi gargadin cewa mummunan mataki zai biyo baya muddin kasar Rasha ta kuskura ta mamaye Ukraine.

Sakataren Harkokin Waje na Birtaniya, Liz Truss, ne ya bayyana hakan yayi wani taron manyan jakadun kungiyar a birnin Liverpool ranar Lahadi.

Kasashen dai, wadanda sune suke juya akalar rabin tattalin arzikin duniya sun ce matukar kasar ta mamaye Ukraine, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukuntata.

Ukraine dai ta kasance a tsaka mai wuya a dangantakar kasashen Gabashi da Yammaci, bayan da ta zargi Rasha da jibge dubban dakaru a shirye-shiryen da take yi na kaddamar da mamaya a kanta.

Sai dai kasar Rasha ta musanta zargin, inda ta ce kawai tsoronta ne ya sa kasashen Yamma suka rikice, tana mai zargin cewa fadada rundunar tsaro ta NATO na barazana gareta, kuma ya saba da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 1991 bayan rushewar Tarayyar Soviet.

Birtaniya dai ta ce tuni ta fara nazari kan irin matakin da za ta dauka na sanya takunkumin karya tattalin arziki, matukar aka mamaye Ukraine din.

Nan gaba kadan ne dai ake sa ran kungiyar ta G7 ta fitar da sanarwa a kan lamarin.

Sai dai a wata kwafin sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani, G7 ta ce tana magana ne da murya daya wajen yin Allah wadai da yadda Rasha ke ci gaba da tara sojoji a kan iyakarta da Ukraine, inda ta yi kira gareta da ta janye.