✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun aika ‘yan ta’adda da yawa lahira —Hafsan Sojin Kasa

Ya ce za su ciga da aika 'yan ta'adda lahira don girbar sakamakon laifin da suka aikata.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, LaftanarJanar Farouk Yahaya, ya ce dakarunsa sun sheka da ‘yan bindiga da dama lahira don su girbi sakamakon abin da suka aikata.

Janar Yahaya ya bayyana haka ne ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Tarayya bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara masa girma.

  1. Cutar Shan-inna ta sake bulla a Jihohi 13 da Abuja
  2. Ta yanke mazakutar mijinta ta soya

Da aka yi masa tambaya a kan umarnin Shugaba Buhari na magana da yaren da ‘yan ta’adda za su fahimta, ya ve “Wannan shi ne abin da muka fara yi tuni.

“Da yawa daga cikinsu mun aika su lahira don su girbi sakamakon laifinsu, kuma za mu ci gaba da yin hakan.”

Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Lucky Irabor, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Isiaka Amao, da Babban Jami’in Leken Asiri (CDI) Manjo-Janar Sunday Adebayo, da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Usman Alkali Baba, na cikin wanda suka halarci karin mukamin nasa.

Kafin nadin nasa, sabon Babban Hafsan na Sojin Kasa ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar ‘Operation Hadin Kai’, mai yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa Maso Gabas.