✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun ba El-Rufai awa 48 ya nemi afuwar ma’aikatan jinyan da ya kora’

Likitoci sun bukaci El-Rufai ya nemi gafarar ma’aikatan jinya ba tare da wani sharadi ba.

Kungiyar Likitoci da Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN), ta bayar da wa’adin awa 48 ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya dawo da ma’aikatan jinya ’yan kasa da da mataki na 14 da kuma neman gafarar ma’aikatan ba tare da wani sharadi ba.

Shugaban kungiyar, Biobelemoye Joy Josiah, ya bayyana matakin gwamnan a matsayin “dabbanci, gidadanci da kuma na Fir’aunanci” wanda har yanzu ake amfani da shi a wannan zamanin a Najeriya.

Josiah ya bayyana cewa tun da farko gwamnan, “Ya saba doka da aiki da tursasawa” wajen yi wa jami’an gwamnatin wadanda suke da shekara 50 da wadanda suke mataki 14 zuwa sama ritaya tare da mayar da ma’aikatan da ke mataki na 01 zuwa 06 zuwa ma’aikatan wucin gadi.

Hakan, a cewarsa, an yi su ba tare da la’akari da dokokin aiki ba.

“Muna kira ga dukkan ma’aikata da ’yan asalin Jihar Kaduna da su sanya ranar Talata, 18 ga Mayu, 2021 a matsayin ranar bakin ciki ga dimokiradiyya kuma ranar makoki, lokacin da zababben gwamna ya yi watsi da kundin tsarin mulkin da ya rantse cewa zai kiyaye, ya rungumi ta’addanci.

“Muna kira ga ’yan asalin Jihar Kaduna, musamman da su tuna da wannan rana ta yadda idan wannan mutumin ya zo yana rokon kuri’un da zai je gidan ritayar tsofaffin gwamnoni – Majalisar Dattawa ko kuma duk wani mukami, kada ku zabe shi.

‘’Ku yi watsi da shi saboda masu Fir’aunanci ba su da wajen zama a inuwar mulkin dimokoradiyya.

“A halin yanzu, muna kira ga mambobinmu a duk fadin kasar nan da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana kuma su jira umarni na gaba a kan wannan batun saboda rauni ga dayanmu, rauni ne ga kowanenmu, sannan rashin adalci a ko ina rashin adalci ne a ko’ina,” inji shi.