✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun ba masu juna-biyu da masu shayarwa tallafin N192.96bn – Gwamnatin Jigawa

Manufar shirin ita ce magance talauci da inganta lafiyar yara

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta kashe sama da Naira biliyan 196 wajen aiwatar da shirinta na ba da tallafi ga mata masu juna-biyu da masu shayarwa daga watan Nuwamban 2021 zuwa Yunin 2022.

Babban Sakatare a Hukumar Raya jihar, Dokta Ibrahim Rabakaya ne ya sanar da haka a Kano ranar Laraba, yayin wani taron kwana uku kan wani shirin tallafa wa matasa ’yan jihar Kaduna.

Ya ce an kirkiro shirin ne a shekarar 2021 bayan irinsa da kungiya Action Against Hunger ta fara yi a jihar.

Dokta Rabakaya ya ce manufar shirin ita ce magance talauci da inganta koshin lafiyar kananan yara.

Babban Sakataren ya ce mata 5,740 ne suka amfana da shirin daga cikin mazabun siyasa 287 da ke jihar.

Ya kuma ce an zabi mutum 20 daga kowacce mazaba da nufin inganta kuzarin yara ’yan kasa da shekara biyar.

Bugu da kari, kowacce daga cikin mata 5,740 din ta sami N32,000 kowanne wata daga tsakanin watan Nuwamban na 2021 zuwa watan Yunin 2022, wanda jimlarsu ya kama Naira miliyan 183 da dubu 680.