✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne saboda ya rika zuwa Daura in mahaifinsa ya bar mulki – Sarkin Daura

Ya ce ce ba shi sarautar ne don saka alhairan da mahaifinsa ya yi wa Daura.

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya ba Yusuf Buhari sarauta a masarautar Daura.

Yusuf dai, wanda shi kadai ne dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, za a nada shi sarautar Talban Daura, kuma Hakimin Kwasarawa ranar Asabar mai zuwa.

Sarkin na jawabi ne a fadarsa ranar Alhamis, yayin bikin nadin sarautar wasu Dagatai guda hudu a masarautar.

A cewarsa, sarautar za ta hana Yusuf din yin sintiri tsakanin Abuja da Yola (garin mahaifiyarsa), alhali Daura ne asalin garinsa.

“Mun ba shi sarautar nan ne saboda saka irin alhairan da Shugaba Buhari ya kawo Daura a matsayin mahaifarsa.

“Ko ba ka kaunar Buhari, ka san Daura a yau ta ci gaba fiye da shekarun baya.

“Saboda mu saka masa, mun ba shi sarautar Talban Daura, wanda shi kuma ya ba babban dansa, Yusuf. Hakan zai hana shi sintiri tsakanin Abuja da Yola in mahaifinsa ya bar mulki.

“Mun samu Jami’ar Sufuri da Kwalejin Fasaha da tituna kusan a kowane layi a Daura. A zahirin gaskiya a yau, Daura ta fi wasu Jihohin na Najeriya ma ci gaba.

“Muna da ’ya’yan Daura da yawa da suka yi fice amma ba sa son alakanta kansu da ita, amma Buhari ya ciri tuta a nan bangaren,” inji Sarkin.

Daga cikin sabbin Dagatan da aka nada har da Armaya’u Bello, wanda aka ba Dagacin Fatautawa, kuma Sarkin Gabas Kwasarawa.