✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta bankado yunkurin tayar da zaune tsaye a Najeriya

Jihohin da ake fako sune Kano da Kaduna da Filato da Ribas da Oyo da Legas.

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta ce ta bankado shirin wasu miyagu da ba a kai ga gano ko su wane ne ba na kokarin tayar da rigimar addini a wasu jihohi.

DSS ta zarge su da yunkurin hada kai da wasu ’yan kasashen waje domin rura wutar rikicin.

Hukumar ta bayyana jihohin Sakkwato da Kano da Kaduna da Filato da Ribas da Oyo da Legas da ma wasu sassa na Kudu maso Gabas a matsayin wuraren da ake yunkurin tayar da rigingimun.

Kakakin hukumar, Peter Afunanya ne ya bayyan haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, “Daga cikin yunkurin akwai na yin amfani da sojin gona wajen kai hari ga wuraren ibada, shugabannin addini, manyan mutane da kuma muhimman wuraren taruwar jama’a.

“Yayin da hukumarmu ke yin iya bakin kokarinta wajen hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen dakile yunkurin nasu, muna rokon jama’a su kaucewa yunkurin don a samu zaman lafiya da ci gaban kasa,” inji sanarwar.

Daga nan sai DSS ta sake kira ga ’yan Najeriya kan su kauce wa dukkan wata makarkashiya da za a yi domin kawo rabuwar kawunansu.