✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun dade muna rokon bankuna su karbi sabbin takardun kudi —CBN

CBN ya ce ya jima yana rokon bankuna da su karbi sabbin kudin amma sun ki.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce ya dade yana rokon bankuna kan su karbi sabbin takardun kudi na Naira da aka sauyawa fasali.

Tun a karshen shekarar da ta gabata dai CBN ya sauya fasalin takardun kudin N200, N500, da kuma N1000, inda ya ce tsofaffin za su daina aiki daga ranar 31 ga watan Janairu.

Sai dai mutane sun nuna damuwa kan yadda sabbin takardun suka yi karanci duba da saura mako biyu wa’adin tsofaffin kudin ya cika.

A bisa haka ne CBN ya bullo da matakai daban-daban, ciki har da hana biyan kudin don samun sabbin takardun kudin.

Babban bankin ya umarci bankunan kasuwanci da su suke saka sabbin kudaden a na’urar cire kudi ta ATM domin rage wa mutane wahala.

A wani shirin wayar da kan jama’a da aka yi a Legas, shugaban sashen harkar shari’a na bankin, Kofo Salam-Alada, ya ce CBN zai sanya doka mai tsauri kan bankunan da ke ci gaba da kin sanya sabbin kudin a ATM dinsu.

Ya ce, “A yau zan iya fada muku cewa CBN a kullum yana fitar da sabbin takardun kudi. Bankuna suna tare da CBN suna karbar kudi. A gaskiya muna rokon bankuna da su zo su karbi kudin nan daga babban bankin kasa.

“Muna da wadannan sabbin takardun kudin Naira a rumbun ajiyarmu kuma muna rokon bankuna su zo su karba.

“Mun gano cewa abubuwa da yawa suna faruwa wanda ya kamata mu bincika, don haka muka dakatar da cire sabbin takardu a bankuna don gudun hada layi don tabbatar da cewa kowa ya samu damar mallakarsu.

“Kazalika, muna da masu sa ido da ke zagaya wa bankuna a yanzu. Na je wasu ATM a safiyar yau kuma na rubuta rahoton abin da ke faruwa.

“Ba wai muna jan hankali mutane don su yi wa bankuna bore ba, muna so ne su yi musu aiki kuma muna baku tabbacin za su yi muku aiki yadda ya kamata.”