✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun daina bai wa miyagun ’yan siyasar Najeriya biza —Birtaniya

Za mu ci gaba da sanya ido akan ’yan siyasar da ke ta da hankali ko kuma tinzira jama’a.

Gwamnatin Birtaniya ta ce miyagun ’yan siyasa a Najeriya su kwan da sanin cewar ba za ta ba su izinin shiga kasarta ba.

Birtaniya ta yi wannan gargadi ne ga ‘yan siyasar Najeriya da ke tinzira magoya bayansu wajen ta da hankali ko kuma rikicin da ke kai ga rasa rayuka, lura da yadda irin wadannan matsaloli ke yi wa shirin zaben shekarar 2023 barazana.

Babbar Jami’ar Diflomaisyar kasar Catriona Laing ta bayyana haka lokacin da ta jagoranci tawagar manyan jami’anta domin ganawa da shugabannin ‘yan kwamitin zartarwar jam’iyyar adawa ta PDP.

Lang ta ce zaben shekarar 2023 na da matukar muhimmanci ga Afirka da kuma duniya baki daya, saboda haka hankalin Birtaniya da kuma kasashen duniya ya karkata akan kasar.

Jami’ar ta ce Birtaniya ta yi matukar damuwa da irin laifuffukan da ke da nasaba da zabe 52 da aka gani a jihohi daban-daban har 22, ciki har da harin da aka kai wa tawagar jam’iyyar PDP a Jihar Borno.

Lang ta ce suna cike da damuwa akan irin wadannan tashe-tashen hankula, saboda haka suka bukaci tattaunawa da shugabannin jam’iyyar akan irin matakan da suka dace a dauka domin tabbatar da ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali.

Birtaniya ta ce yana da wahala mutane su fito su yi zabe muddin suna fuskantar takala ko barazana, yayin da wadannan abubuwa na iya shafar kimar zaben baki daya.

Lang ta ce za su ci gaba da sanya ido akan ’yan siyasar da ke ta da hankali ko kuma tinzira jama’a ta da hankalin wajen amfani da kafofin yada labarai daga kowacce jama’iyya domin daukar mataki akansu.