✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun daina kai wa CBN ajiyar kayan zabe —INEC

Daga yanzu CBN ba zai sake ajiye kayan zaben ba tun daga kan zaben gwamnan Jihar Ekiti.

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ba za ta sake kai kayan zabe masu muhimmanci ajiya ba a Babban Bankin kasar (CBN).

Da yake magana yayin wani taron kara wa juna sani a Abuja ranar Asabar, shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce daga yanzu CBN ba zai sake ajiye kayan zaben ba tun daga kan zaben gwamnan Jihar Ekiti da za a gudanar ranar 18 ga watan Yuni.

Bisa al’ada, INEC kan kai kayan zabe kamar takardun jefa kuri’a da takardun rubuta sakamako da abin jefa kuri’a na masu lalurar ido ajiya a CBN kafin fara kada kuri’ar yayin zabuka a Najeriya.

Sai dai babu tabbas ko matakin na da alaka da ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Gwamnan CBN Godwin Emefiele na son ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Ya ce “muna duba yadda za mu inganta gudanar da ayyukan, saboda haka ba lallai ne hakan yana da alaka da abin da ke faruwa a CBN ba. Manufarmu ita ce a kodayaushe mu inganta da kuma gudanar da ayyukanmu da kanmu.

“Ba za mu yi amfani da CBN ba a zaben Ekiti. Za a kai kayan zaben daga ofishinmu na Abuja zuwa filin jirgi sannan a kai su ofishinmu na jiha,” a cewar Farfesa Yakubu.

Shugaban na INEC ya kuma ce hukumar ta amsa bukatun Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta hanyar gabatar mata da bayanan asusun banki da sauran bayanan kudaden jam’iyyun siyasa.

A bayan nan ne dai EFCC ta kaddamar da bincike kan kudaden jam’iyyun siyasar kasar nan 18 da suka yi wa rijista da kuma masu neman takarar shugabancin kasar nan, biyo bayan wasu makudan kudade da aka biya na fam din takara da masu neman tsayawa takarar mukamai daban-daban suka yi.