✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun dakatar da Rasha daga Hukumar Kare Hakkin Bil’adama —MDD

A karo na biyu kenan a tarihi da ake dakatar da wata kasa daga Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta MDD.

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da Rasha a matsayin mamba a Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Wannan na zuwa ne yayin da Babban zauren Majalisar Dinkin Duniyar ya kada kuri’ar dakatar da Rashan a wani zama da ya yi a New York.

Matakin ya biyo bayan tuhumar da ake ma Rasha cewa sojojinta na aikata laifukan yaki a Ukraine.

Kafin a kada kuri’a, jakadan Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya Sergiy Kyslytsya ya tuhumi Rasha da aikata munanan laifuka – musamman bayan kashe-kashen da ake tuhumar Rashar da aikatawa a garin Bucha.

Daga cikin kasashe 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya, 93 sun kada kuri’ar amincewa da dakatar da Rasha kamar yadda Amurka ta bukata, yayin da kasashe 24 suka ki amincewa da matakin, 58 kuma suka yi rowar kuri’arsu.

Wakilin Rasha Gennady Kuzmin ya yi tir da kuri’ar, sannan kuma wasu kasashe, ciki har da Koriya ta Arewa da Syria sun mara ma sa baya.

Sauran kasashen da suka ki goyon bayan dakatar da Rasha sun hada da China wadda ke zama aminiya sosai ga Moscow, sai kuma Iran da Kazakhstan da Cuba da Belarus.

Da dama daga cikin kasashen Afrika sun kaurace wa zaman kada kuri’ar duk da matsin lamnbar da Rasha ta yi musu, kamar Afrika ta Kudu da Senegal.

Su ma kasashen Brazil da Mexico da India sun yi rowar kuri’arsu.

Kuri’ar ta nuna karara yadda kawunan kasashen duniya suka rarrabu dangane da ladabtar da Rasha kan hare-harenta a  Ukraine.

A karo na biyu kenan a tarihi da ake dakatar da wata kasa daga Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, inda aka fara daukar makamancin wannan mataki kan Libya a shekara ta 2011.

Dokar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, dole ne a samu kashi biyu bisa uku na mambobin da suka amince kafin dakatarwar ta tabbata, amma banda kidayar kasashen da suka yi rowar kuri’arsu.