✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun dakile hari a Kano da ka iya zama mafi muni a tarihin Najeriya —Janar Irabor

Mun kwace makamai masu yawan gaske da miyagu ke kokarin yin amfani da su a sassan kasar nan ciki har da Abuja.

Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce dakarun soji sun dakile wani yunkurin kai hari a Jihar Kano, “wanda ka iya zama mafi muni a tarihin kasar.”

Janar Irabor ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya bayyana cikin wani shiri na neman ’yan Najeriya su ci gaba da kyautata zato ga kasar nan a yayin bikin Ranar Dimokuradiyya da kafar talabijin ta Channels da dauki nauyi.

Ya ce an dakile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari kan wani cocin Katolika a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ’yan bindiga suka bude wa masu ibada wuta.

Aminiya ta ruwaito cewa, akalla mutum 40 ne aka tabbatar da sun rasu a yayin harin da aka kai, inda sama da mutum 120 kuma suka samu raunuka yayin harin da aka kai a Cocin St. Francis Catholic a garin Owo a ranar Lahadi, 5 ga watan Yunin 2022.

Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan ta’addan kungiyar ISWAP ne suka kai hari kan Cocin a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola da yake magana da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa a ranar Alhamis ta makon jiya.

Da yake magana dangane da harin na Owo, Janar Irabor ya ce, “Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kadai da aka kai harin Coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar dakile harin da ka iya zama mafi muni a tarihin kasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da su.

Wakilinmu ya ruwaito Janar Irabor yana cewa sun kwace kunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke kokarin yin amfani da su a sassan kasar nan ciki har da Abuja.

Janar din ya kara da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a fadin Najeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara daya da ta wuce.”