✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun dauki matakan kawo karshen karancin mai —NNPC

NNPC ya tabbatar da cewar jirage makare da man fetur na dab da isowa Najeriya.

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya tabbatar da cewa, kamfanin ya samar da matakan shawo matsalar karancin man fetur da ake fama da ita yanzu a fadin kasar nan.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kwamitin Majalisar Wakilai kan albarkatun man fetur a ranar Laraba.

Kyari ya bayyana karancin man a matsayin wata matsala da ba a yi tunanin samun ta ba, amma ya ce jirage makare da man fetur na gab da zuwa Najeriya.

A cewarsa, janye jiragen mai guda biyar da aka yi dauke da man fetur din, shi ne ya haifar da karancin man, wanda hakan ya shafi zirga-zirgar ababen hawa.

Sai dai ya ce NNPC ya shigo da adadi mai yawan gaske daga kasar waje wanda zai cike gibin tare da dawo da daidaituwar al’amuran man fetur a kasar nan.

Kazalika, Kyari ya ce NNPC ya yi yarjejeniya tare da hadin gwiwa da masu shigo da man fetur don kawo ishasshen mai da zai kawo karshen matsalar man da ake fuskanta.

Tun da farko, shugaban kwamitin, Abdullahi Mahmoud, ya ce dole ne kamfanin NNPC ta tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansa yadda ya dace.

Ya ce, abin da ya faru ya jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, wanda ke iya ta’azzara abubuwa da dama saboda sakacin kamfanin.

Matsalar karancin man fetur ta yi muni musamman a Abuja, Legas da sauran wasu jihohin, har ta kai ga ana sayen litar mai a kan N600 a wasu jihohin.

Lamarin dai ya jefa dumbin mutane cikin mawuyacin hali na gaza yin zirga-zirga saboda tsadar ababen hawa yayin sufuri.