✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun Fatattaki Cutar Barcin Da Ta Addabe Mu —Uganda

Ma’aikatar lafiya ta Uganda, ta ce ta samu nasarar kawar da cutar barci da ta dade tana addabar al’ummar kasar. Ma’aikatar ta shafinta na Twitter…

Ma’aikatar lafiya ta Uganda, ta ce ta samu nasarar kawar da cutar barci da ta dade tana addabar al’ummar kasar.

Maaikatar ta shafinta na Twitter ta ce, wannan nasara ta samu ne dalilin sanya ido sosai, da kokarin magance Kudan Tsando da ke haddasa cutar, hadi da nazartar mutane da dama da ke dauke da kwayar cutar da ta yi.

Ta ce cutar ta dade tana addabar yankin Arewacin Kogin Nilu, inda ta nukurkusa kimanin mutane miliyan biyu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kasashe 36 ne a yankin Afirka ke fama da cutar ta barci, kuma akwai bukatar su mike tsaye domin kau da ita, tun kafin ta gama yi musu illa.

Ta kuma ce da zarar mutum ya ji  yana yawan jin gajiya da zazzabi mai zafi da ciwon kai hadi da ciwon gabobi, to ya gaggauta zuwa asibiti.