✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun gaji da gafara sa kan harkar tsaro’

Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da kara tabarbarewa a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bukaci Gwamnati Tarayya da ta fito da…

Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da kara tabarbarewa a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bukaci Gwamnati Tarayya da ta fito da nagartattun tsare-tsaren magance matsalar cikin gaggawa.

Shugaban NLC na kasa Kwamared Ayuba Wabba ya nuna takaicinsa kan yadda kalubalen tsaro hadi da annobar coronavirus ke ci gaba da yin mummunar illa ga harkokin noma da kasuwanci.

Ayuba Wabba ya ce gwamnati ta daina alkawura kan harkar tsaro kawai ta yi abin da ya dace, domin, “Kusan duk nasarar da aka samu a baya yanzu tana neman disashewa.

“Ya kamata gwamnati ta sauya salonta musamman wajen yaki da ‘yan tada kayar baya. A irin wadannan yankunan, kusan duk manoma an tarwatsa su kuma ba su da damar yin harkoki”.

A jawabinsa ga ‘yan jarida a ranar Litinin a Abuja, Wabba ya ce hakan na barazana ga harkar samar da abinci a kasa sakamakon yadda manoman suka koma ‘yan gudun hijira a kasar.

Da yake zargin gwamnati da gazawa wajen yin abinda ya dace, yace kungiyar ba za ta nade hannu tana kallon lamarin na dada tabarbarewa ba.

“Ya zama tilas mu fito mu yi kira ga gwamnati mu kuma fada mata gaskiya kan hakikanin abin da ke faruwa a harkar tsaro”, inji shi.