✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun haka wa ’yan bindiga rijiyoyi 138 —Gwamnan Zamfara

''Mun san cewa jami’an tsaro ba za su iya dakatar da su ba'', inji Matawalle.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta gina rijiyoyi 138 a sansanonin ’yan bindiga a Jihar da ke fama da matsalar tsaro.

Matalle ya bayyana haka ne a yayin da yake jaddada muhimmancin yin sulhu da ’yan binidgar da suka addabi jihar domin a samu zama lafiya.

“Mun san cewa jami’an tsaro ba za su iya dakatar da su ba, mafita ita ce zaunan tattaunawa.

“Mun haka rijiyoyi 138 a sansanin ’yan bindiga, kuma ba za mu daina ba har sai mun samar da zaman lafiya,” inji gwamnan, wanda ya cewa wasu na zarginsa da sassauta wa ’yan bindiga.

Ya yi bayanin ne a ganawarsa da malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi wanda ya shiga dazukan Jihar Zamfara domin yi wa ’yan bindiga wa’azi.

Sheik Gumi ya shaida wa gwamnan cewa jagororin ’yan bindiga sun shaida masa cewa zaman lafiya ba zai wanzu ba a Jihar har sai ’Yan Sakai da sojoji sun daina kashe Fulani a Jihar.

“Kwamandojin ’yan bindiga sun shaida min cewa sojoji na kai hare-hare cikin daji kuma hakan ya shafi kowane dangi, kuma a cewarsu dole ne a daina.

“Game da wannan akwai ra’ayoyi mabambanta; wasu na ganin bai kamata gwamnati ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, wasu kuma na ganin kawai a murkushe su.

“Abin da muka fahimta shi ne mutanen nan ba su da ilimi ko kadan. Amma in har za a ja hankalinsu to ina ganin za su ba da gari,” a cewar malamin.

Sheikh Gumi ya ce yadda sojoji ke kai hari a kan ’yan bindigar ba zai kawo karshen matsalar ba.

Malamin ya kara da cewa abin da ya fi dacewa shi ne a yi zama tare don nemo mafita tare da masu ruwa da tsaki.

Ya shawarci Gwamna Bello Mohammed Matawalle, kan ya tattauna da su ba tare da wani a shamaki ba, saboda a tunaninsa hakan ne ya kawo rashin fahimta a lokutan baya.

Sannan ya ba da shawarar cewa a fito da tsari ga wadanda suka amince su ajiye makamansu ta yadda za a sama musu abun yi kamar yadda gwamnati ta yi a yankin Neja Delta, don samar da zaman lafiya.