✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kaddamar da yaki da ’yan bindiga —Gwamnan Binuwai

Ortom ya ce sulhu ko yafiya ga ’yan bindiga a jiharsa ya zama tsohon labari

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ya ayyana yaki tsakanin Gwamnain Jihar da ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda a Jiharsa.

Ortom ya ce gwamnatin sa ba za ta sake tattaunawa ko yin afuwa ga masu aikata laifuka ta kowace irin fuska ba.

Ya bayyana hakan ne yayin jana’izar Dokta Terkura Suswam, wan tsohon gwamnan Jihar, Sanata Gabriel Suswam wanda ’yan ta’adda suka kashe.

An kashe Dokta Terkura Suswam ne a gidansa da ke garin Anyiin a Karamar Hukumar Logo ta Jihar, tare da mai taimaka masa, Solomon Tarnor, kuma tuni aka binne su a karshen mako.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa, ta hanyar Kwamitin Tsaro na Jiha, ta ayyana yaki a kan maharan da sauran masu aikata laifuka a fadin jihar, yana mai cewa duk daren dadewa, za a ci galaba kan miyagun.

Ya bayyana marigayi Suswam a matsayin dattijo wanda za a ci gaba da tuna shi da kyawawan ayyukansa, wanda ya rasu ne a kan gwagwarmayar kawo zaman lafiya, cigaba da bunkasa tattalin arzikin al’ummarsa.

“A cikin Anyiin kadai, muna da Ashi Polytechnic, Babbar Kasuwar Ashi, kamfanin shinkafa da banki kuma wadannan sune abubuwan da suke jan hankalin masu saka jari su zo saboda gwamnati ba ta da karfin daukar dukkan mutane aiki ita kadai.

“Abin da Dokta Suswam ya hango ke nan, amma abin takaici, sai ya gamu da ajalinsa a nan garin Anyiin, a yayin da yake kokarin bunkasa cigaban tattalin arzikin al’umma,” inji gwamnan.

Ya kuma koka da cewa ayyukan miyagun na iya mawadata dawowa gida su zuba jari, saboda tsoro. Ya kuma yi kira da cewa kada mutane su rudu da wannan lamarin.