✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kafa kwamitin tattara sakamakon zaben shugaban kasa —INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta kafa kwamitin tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi, karkashin jargorancin shugaban hukumar, Mahmood Yakubu. INEC ta…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta kafa kwamitin tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi, karkashin jargorancin shugaban hukumar, Mahmood Yakubu.

INEC ta ce zauren taro na Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa (ICC) da ke Abuja, shi ne zai zamo cibiyar tattara sakamakon babban zaben na 2023.

Hakan ya bulla ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye ya fitar.

Hukumar ta ce daga ranar Juma’a ce za ta fara karbar katinan zabe na dindindin daga ofisoshinta da ke mazabu 8,809 da ke fadin Najeriya ga wadanda ba su karba ba.

INEC ta sanya ranar 12 ga watan Disamba, 2022 zuwa 22 ga Janairu, 2023 a matsayin wa’adin karbar katinan zaben na dindindin.

“Duk wadanda suka sabanta katinansu da suka bata, ko suka lalace, ko ba su karba ba tun na zaben 2019 da suka yi, to su je ofisoshinmu na mazabu su karba,“ a Okoye.