✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kama bako da kullin hodar iblis 105 daga Brazil —NDLEA

An gano hodar ce bayan da jami'an NDLEA suka tsananta bincike cikin kayan wanda ake zargin.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama kullin hodar iblis 105 a cikin kayan wani wanda ya dawo daga kasar Brazil a Babban Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya sanar ranar Lahadi a Abuja cewa sun kama wanda ake zargin ne ranar Kirsimeti.

Ya ce wanda ake zargin na daga cikin fasinjojin da suka dawo daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil.

A cewarsa, bayanan sirrin da suka samu sun taimaka wajen kama wanda ake zargin a filin jirgin.

Ya ce, saura kiris ya sha sakamakon babu abin da suka gano a binciken farkon da suka yi masa.

Da aka tsananta bincike a kansa karo na biyu, sai aka gano hodar iblis din da yake dauke da ita, in ji jami’in.

Shugaban NDLEA na Kasa, Birgediya-Janar Buba Marwa (Murabus), ya sha nanata cewa ba za su raga wa masu fataucin miyagun kwayoyi ba ko’ina suke a fadin kasa.

(NAN)