✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kama kilogiram 374.47 na Tabar Wiwi cikin wata 2 a Kano – NDLEA

Hukumar ta kuma ce ta kama dilolin 131 a tsakanin watannin

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Jihar Kano ta ce a tsakanin watannin Janairu da Fabrairun 2022, ta kama Tabar Wiwin da nauyinta ya kai kilogiram 374.34 sannan ta kama dilolinta 131.

Kwamandan hukumar a Jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ne ya bayyana hakan a Kano ranar Laraba.

Ya kuma ce baya ga wadannan, hukumar ta kuma sami nasarar kama kilogiram 1.3 na maganin Codeine da kilogiram 180.585 na kwayar Diazepam da kuma giram 100 na kwayar Raphenol da sauran miyagun kwayoyi tsakanin lokacin.

Kazalika, Kwamandan ya ce ko a watan Maris din nan sai da hukumar ta lalata wasu gonakin Wiwi a kananan hukumomin Bebeji da Dawakin Kudu sannan ta kama wasu mutum biyu da take zargi da hannu a gudanar da su.