✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun karbi kararraki 1,161 a Katsina a bara  —NSCDC

Mun magance laifuka guda 256 da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade, da sauran laifuka.

Hukumar Tsaro mai ba da kariya ga fararen hula da kuma kadarori gwamnati a Najeriya da ake kira “Cibil Defence” (NSCDC) ta sanar da samun kararraki 1,161 na masu aikata laifuka da kuma wadanda suka shafi na farar hula a Jihar Katsina a shekarar 2021 da ta gabata.

Kwamandan rundunar a Jihar, Mohammed Sanusi Bello ne ya bayyana hakan a hedikwatarta da ke birnin Dikko a ranar Juma’a, yayin da yake yi wa ’yan jarida bita kan ayyukan da suka gudanar a shekarar 2021.

“A cikin wadannan adadi, mun yi maganin laifuka guda 256 da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane, sata, shan muggan kwayoyi, fyade, lalata da sauran laifukan da suka sabawa dabi’a.

“Rundunar a cikin wannan shekarar da aka yi bitar ta samu tare da kula da jimillar shari’o’in farar hula daban-daban har 905, wadanda suka hada da basussuka, rashin fahimtar juna, batutuwan da suka shafi filaye, rikicin manoma da makiyaya, rikicin cikin gida da sauransu.”.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa, sun yi wani gagarumin yunkuri na kare muhimman kadarorin kasa da kayayyakin more rayuwa daga hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa, wanda ya ce jami’ansu za su ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

“Mun kama wani Sunday Isaac da Hamisu Salisu da ke cikin garin Katsina dauke da buhunan tabar wiwi 173 da kuma wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Abdulrashid Muhammed, haka kuma rundunar ta samu nasarar kwato kudi har naira miliyan 54.3 tare da mika su ga masu korafin lamuran basussuka da sauran abubuwan da ke da alaka da haka a duk sassan jihar.

Kazalika, Kwamanda Muhammed Sanusi ya yi kira ga jama’a da su rika taimaka wa jami’an rundunar tare da sauran jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai  akan lokaci domin dakile kalubalen tsaro yadda ya kamata a jihar.