✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe $1bn wajen kwato yankunan da ’yan ta’adda suka mamaye – Buhari

An karrama Buhari da lambar yabo kan karfafa zaman lafiya.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya ta kashe sama da Dala biliyan daya wajen sayen makaman da ta yi amfani da su wajen yaki da ’yan ta’adda tun 2015.

Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata sa’ilin da yake jawabi a wajen Babban Taron Zaman Lafiya na Afirka na 2023, da ya gudana a birnin Nouakchott, Jamhuriyar Musulunci ta Murtaniya.

Shugaban wanda aka karrama da lambar yabo ta “Karfafa Zaman Lafiya a Afirka” a Abu Dhabi, ya ce akwai bukatar a rungumi dabi’ar karrama juna da mutuntawa a makarantu, musamman kuma a tsakanin matasa.

Haka nan, ya yi kira ga shugabanni da su bai wa rayuwar matasa muhimmanci ta hanyar horar da su sana’o’in hannu domin maganin zaman kashe wando.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, Buhari ya ce dole a ba da himma wajen hana ta’ammali da kananan bindigogi da sauran makamai a cikin al’umma.

Kana ya bukaci yayin taron kasashen Afirka na gaba, a dauki matakin lalubo hanyar magance matsalolin da ke ci gaba da yi wa kasar Libiya tarnaki wanda hakan ya sa kasar ta zama dandalin ta’ammali da makamai da mayakan ketare.

“Ta’addanci da fashin daji da sauran manyan laifuka na ci gaba da zama kalubale ba ga Afirka kadai ba, amma ga zaman lafiya da tsaron duniya baki dayanta.

“Wannan matsalar ta zama kashin makogwaro ga tattalin arziki da bunkasar al’umma,” in ji Buhari.

Ya kara da cewa kafewar Tafkin Chadi ta haifar wa al’ummar yankin rasa hanyoyinsu na samun masarufin rayuwa wanda hakan ya yi sanadiyyar jefa dimbin matasan yankin cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A karshe, Buhari ya yi godiya ga Majalisar Zaman Lafiya ta Abu Dhabi karkashin jagorancin Shaykh Abdallah Bin Bayyah, bisa karrama shi da ta yi da lambar yabon.