✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe N1.5bn wajen shirya jarrabawar 2020 —WAEC

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta ce ta kashe kimanin Naira biliyan daya da rabi wajen shirya jarrabawar kammala sakandire ta 2020.…

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta ce ta kashe kimanin Naira biliyan daya da rabi wajen shirya jarrabawar kammala sakandire ta 2020.

Shugaban ofoshin hukumar a Najeriya, Mista Areghan Patrick shine ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake kare kasafin kudin hukumarsa a cikin kasafin kudin 2021 a gaban Kwamitin Ilimin Bai Daya na Majalisar Wakilai ranar Juma’a.

Areghan ya ce sama da dalibai miliyan daya da rabi ne suka zauna jarrabawar a bana, yayin da mutum 80,000 suka yi aikin makin sakamakonta.

Shugaban ya kuma ce dukkan daliban da suka zana jarrabawar sun biya N13,900 a matsayin kudaden rijista, inda ya ce kudin rijistar da na gudanarwa ne kawai suka shiga lalitar hukumar.

Sai dai ya ce WAEC ba hukumar tattara kudaden shiga ba ce, ta kan karbi kudade ne kawai daga hannun dalibai domin shirya musu jarrabawa kuma ba ita take amfana da su ba.

Shugaban hukumar ya kuma koka kan cewar hukumar ba ta samun isassun kudaden gudanarwa, yana mai cewa yanzu haka suna da gibin Naira biliyan bakwai.

Daga nan sai ya roki majalisar kan ta tabbatar an fitar da dukkan kudaden da aka ware mata a kasafin kudin na badi domin ta tsaya da kafarta.

Da yake tsokaci, shubaban kwamitin majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ya yaba da muhimmin aikin raya kasar da WAEC take yi, yana mai ba su tabbacin ci gaba da basu cikakken hadin kai.

Sai dai kuma ya kalubalanci hukumar kan ta kara inganta hanyoyin samar da kudaden shiga ta hanyar yin koyi da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta JAMB.