✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe N2bn wajen gina sabbin shaguna 1,050 a babbar Kasuwar Kebbi — Bagudu

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku-Bagudu ya ce Jihar ta kashe sama da Naira miliyan biyu wurin sabunta ginin shaguna 1,050 da gobara ta cinye a…

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku-Bagudu ya ce Jihar ta kashe sama da Naira miliyan biyu wurin sabunta ginin shaguna 1,050 da gobara ta cinye a babbar kasuwar Birnin Kebbi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a kasuwar ta Birnin Kebbi, yayin da yake mika sama da shaguna 350 da aka sake gina su ga masu ainihin shagunan, wadanda suka cika shuradan da gwamnatin jihar ta gindaya musu.

Atiku-Bagudu, wanda kwamishan mahalli da gidaje na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Sadiq-Yelwa, ya wakilta a wurin mika shagunan, ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar mayar wa da masu ainihin shagunan shagunansu.

“Duk wanda ya mallaki shago kafin faruwar gobarar za a sabunta masa da wani sabon shagon, haka kuma dukkan wanda ya gaji shago daga wurin mahaifansa kuma yana gudanar da harkokin kasuwancinsa a ciki shi ma za a maida masa.”

Gwamnan ya bukaci wadanda suke da bukatar siyan sabbin shagunan da su bi tsarin da ya dace wurin mallakar shagunan.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan kasuwar cewa, gwamnati ta himmatu ainun wurin ganin an saki sauran shagunan nan bada jimawa ba.

Atiku-Bagudu ya bukaci Hukumar Kula da kasuwar da ta tabbatar da gudanar da rabon shagunan kasuwar yadda ya kamata ba tare karya tsarin da aka shimfida ba, ya kuma bukaci ’yan kasuwar da su yi amfani da shuganan yadda ya kamata ta yadda za su ci moriyarsu.

Ana iya tuna cewa, a watan Dasumbar 2016 ne gobara ta lakume shaguna bila adadin da dukiya mai tarin yawa a babbar kasuwar ta Kebbi.