✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe ’yan bindiga 54, mun cafke masu fyade 266 a Katsina —’Yan sanda

Rundunar ta kwace bindigogi guda 95 daga hannun ’yan bindiga, amma ta yi asarar ’yan sanda biyar a musayar wuta

’Yan sanda saun aika ’yan bindiga 54 lahira tare da cafke masu fyade 266 a Jihar Katsina a shekarar 2022 mai bankwana.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Shehu Umar Nadada, ya ce rundunar ta kwace bindigogi guda 95 daga hannun ’yan bindiga, amma ta yi asarar ’yan sanda biyar a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a shekarar.

“A ci gaba da yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da satar dabobbi, mun kashe ’yan bindiga 54 a arangama daban-daban, yayin da ’yan sanda biyar suka rasu,” in ji Kwamishinan ’yan sandan.

Ya ce rundunar ta damke mutum 241, ciki har da ’yan bindiga da masu kai musu bayanai da barayin dabobbi, kuma an gurfanar da 239 cikinsu a kotu, 16 kuma ana ci gaba da bincike a kansu.

“Mun kama ’yan fashi 177 kuma an gurfanar da 169 a kotu, mutum takwas kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

“Mutum 266 sun shiga hannu kan zargin aikata fyade kuma tuni muka aike da 260 daga cikinsu kotu,” in ji shi.

Nadada ya shaida wa ’yan jarida a taron karshen shekara a hedikwatar rundunar da ke Katsina a ranar Juma’a cewa sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda 14, kirar gida guda 81, kwanson harsasai 47 da kuma sauran makamai.

Mutum 989 kuma na kotunan jihar suna jiran a yanke musu hukunci kan laifukan da aka gurfanar da su.

Kwamishinan ya ce rundunar ta kwato dabobbi 1,092, shanu 705 da tumaki da awaki 370 da sauransu.

Ya gode wa Sufeton-Janar na ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki na jihar kan yadda suke bai wa sha’anin tsaro muhimmanci.