Mun kashe ’Yan Najeriya 38 da ke taimakon Ukraine a yaki —Rasha | Aminiya

Mun kashe ’Yan Najeriya 38 da ke taimakon Ukraine a yaki —Rasha

Shugaban Rasha, Vladmir Putin
Shugaban Rasha, Vladmir Putin
    Ishaq Isma’il Musa

’Yan Najeriya 38 da ke taimaka wa Ukraine a yakin da take da mamayar Rasha ne suka mutu a fagen daga, a cewar wani kundi da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta wallafa, wanda ke dauke da adadin sojojin haya da suka mutu.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa ’yan Najeriya 38 daga cikin 85 da suka je taimaka wa Ukraine ne suka mutu, a yayin da 35 suka koma gida, 12 na nan suna ci gaba da yaki a matsayin sojojin haya.

Wata sanarwa daga Ma’aikatar Tsaron ta Rasha ta ce duk kuwa da dimbim kudade da gwamnatin Ukraine ke biyan sojojin hayan hakan bai hana dakarun Rasha sun mayar da su tarihi ba

Sanarwar ta ci gaba da cewa tun da aka raba rana tsakanin Rasha da Ukraine, mutane dubu 1 da dari 8 da 31 suka isa kasar daga Poland kawai da zummar yin aiki a mstayin sojojin haya, inda daga cikin su, 378 sun kwanta dama, a yayin da 272 suka arce zuwa kasashensu na asali.

A cewar Ma’aikatar Tsaron ta Rasha, akwai sojojin haya dubu 3 da 321 da ke da rai, wadanda ba a kai ga kame su ba, ko kuma ba a kashe ba, tana mai cewa daga ranar 17 ga watan Yuni, mayaka ‘yan kasashen waje dubu 1 da dari 956 ne Rasha ta kashe, a yayin da sama da dubu 1 da 700 suka arce zuwa kasashensu.