✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kwace miyagun kwayoyi na N420bn a wata 21 – NDLEA

NDLEA ta ce ta yi kamen ne a sassan Najeriya daban-daban

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama miyagun kwayoyin da kimarsu ta kai ta kusan Naira biliyan 420 tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Satumban da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan yayin wata zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Abuja.

Ya ce hukumar ta kuma sami nasarar cafke mutum 19,341 da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyin, ciki har da manyan dilolinsu kimanin su 28, inda kuma ya ce kwanan nan za su hada alkaluman watan Satumban da ya wuce.

Femi ya kuma ce hukumar ta sami nasarar kotuna su yanke wa mutum 3,111 hukunci, yayin da wasu 3,232 har yanzu ke zaman jiran a yanke musu hukuncin.

Bugu da kari, Kakakin ya ce hukumar ta sami nasarar gyara halin mutum 12,326 a tsawon wannan lokacin.

A cewarsa, “Ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya ya karu da kaso 14.4 cikin 100 a wannan lokacin, inda mutum 12,326 muka sami nasarar gyara musu hali a wuraren da muka tanadar saboda haka.

“An kuma kulle asusun bankuna sama da 600, sannan an kwace kadarorin dilolin kwaya da dama daga watan Janairun 2021 zuwa watan Satumban da ya gabata.

“Mun kuma kwace motocin alfarma da manyan gidaje yanzu haka ana dab da kwace su don a damka wa gwamnati, sannan mun kama miyagun kwayoyi na sama da Naira biliyan 420,” inji shi.

Kakakin ya ce lokaci ya wuce da dilolin kwaya za su rika buya suna fakewa da sunan wasu, sannan ya ce hukumar za ta ci gaba da tona asirinsu matukar suka ki su tuba. (NAN)