✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun lalata gonakin Tabar Wiwi masu fadin hekta 2 a Imo – NDLEA

Hukumar ta lalata gonakin ne a Owerri

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta lalata gonakin Tabar Wiwi da fadinsu ya kai hekta biyu a unguwar Umuguma da ke Karamar Hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo.

Kakakin hukumar a jihar, Alhaji Shehu Lamua, ne ya shaida wa manema labarai hakan a Owerri, babban birnin jihar.

Ya ce babban makasudin kai samamen shi ne na yunkurin ganin an rage yawan ta’ammali da miyagun kwayoyi yadda ya kamata.

A cewar kakakin, tun a shekarar 2013, NDLEA ta matsa kaimi wajen wayar da kan al’ummar Jihar kan illar ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Sai dai ya yi korafin cewa jihar ta Imo ba ta da isassun kayan da za a yi amfani da su wajen magance shan kwayoyin, inda ya ce matsalar ta yi girman da a Najeriya dole a hada karfi da karfe kafin a iya yakarta.

Alhaji Shehu ya kuma kira ga gwamnatin jihar da ma’aikatan lafiya, masu hannu da shuni da sauranasu ruwa da tsaki da su taimaka wajen kawo karshen matsalar a jihar.