✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun raba wa jihohi rigakafin Haukan Kare miliyan 2.6 – Gwamnatin Tarayya 

Rigakafin dai kyauta ce, kuma ana sa ran kowanne kare ya samu

Gwamnatin Tarayya ta ce raba wa jihohi 36 kwalaben rigakafin cutar Haukan Kare guda miliyan biyu da dubu dari shida don kowane kare ya samu.

A sakamakon haka, kowacce jiha za ta samu kwalaben da ba su gaza 30,000 ba saboda kowanne kare ya samu a masa rigakafin kuma kyauta ne.

Dokta Maimuna Abdullahi Habib, Shugabar Babbar sashin kula da lafiyar Dabbobi ta Najeriya ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Gombe a lokacin da tawagar suka ziyarci Sakandare Gwamnati ta ’yan mata ta Doma da ke Gombe.

Sun je makarantar ne don wayar wa daliban kai kan illar cizon mahaukacin kare.

Da take amsa tambayoyi kan ko cizon mahaukacin karen yana warkewa, ta ce a’a, amma ana magance shi 100 bisa 100.

Ta kuma cewa suna sa ido matuka kan rigakafin cizon karen don tabbatar da cewa kowanne kare an yi masa, gudun kar ya kamu da cutar.

Dokta Maimuna, ta kuma ce bikin na bana na jihar Gombe ya gudana ne a karamar hukumar Dukku saboda an samu rahoton mutuwar mutane hudu da kare ya ciza a yankin.

Sai dai ta ce duk da irin kudin da aka kashe wajen sayen rigakafin da kuma raba shi kyauta, hakan bai sa an zayyana wani hukunci kan wadanda suka bijire wa amfani da shi ba.