✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun raba wa gwamnoni tan 70,000 na kayan abinci —Sadiya Farouk

Sadiya Umar-Farouk ta ce ta raba wa jihohi 36 tan 70,000 na kayan abinci lokacin kullen COVID-19

Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa Sadiya Umar-Farouk ta ce ma’aitakarta ta rabawa gwamnonin jihohi 36 tan 70,000 na kayan abinci lokacin kullen annobar COVID-19.

Ta bayyana hakan ne yayin wata hirarta da Sashen Hausa na BBC ranar Talata a jihar Zamfara, tana mai cewa sun kuma raba tireloli 145 na shinkafa ga jihohin.

A cewar ministar, “Ni na yi aiki na, mun rabawa gwamnonin jihohi kayan abinci kuma ido na ganin ido muka raba kowa yana gani.

“Mun raba musu sama da tan 70,000 na kayan abinci. Shinkafar da muka samu daga Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa ma mun rabawa jihohin, hatsi ne kawai muka rabawa jihohi 24 saboda ba kowacce jiha ce take amfani da hatsi a matsayin abinci ba.

“Dalilan da wasu gwamnonin kuma suka bayar na kin raba kayan wai suna tsammanin sake dawowar annobar COVID-19 a karo na biyu wannan kuma su ta shafa.

“Ya rage masu su amsa wannan tambayar, ni dai na raba musu kuma ina da shaidar hakan, gaskiya ta riga ta fito fili,” inji Sadiya.

Ministar ta kara da cewa ma’aikatarta ta umarci gwamnonin su rabawa al’ummar jihohinsu tun a lokacin kamar yadda shugaba Buhari ya ba da umarni.

A kan ko gwanatin za ta sake duba yuwuwar ba jihohin wasu kayan tallafin kasancewar zauna-gari-banza sun kwashe wadancan kuwa, Sadiya ta ce dole sai sun tattauna kafin yanke shawara a kai.