Kungiyar da ta jagoranci shirya zanga-zangar #EndSARS ta ce ta samu gudunmawar makudan kudade daga wasu kasashen waje da yawansu ya kai Dalar Amurka 400,000.
Jimlar kudaden dai sun haura Naira miliyan 150 a kudin Najeriya.
- Masu zanga-zanga sun dakawa kayan tallafin COVID-19 wawa a Osun
- Zanga-zangar #EndSARS ta jawo asarar biliyan 400 a Legas
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadakar kungiyoyin karkashin Feminist Coalition suka fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar Juma’a.
Kungiyar ta bayyana cewa ta tara gudummawar kudaden da ta samu daga sassan duniya daban-daban kuma har yanzu ba ta kammala kashe su ba.
Sai dai ta ce daga yanzu ba za ta sake karbar wata gudummawar kudi da sunan #EndSARS daga kowa ba.
Daga nan sai ta bukaci matasa da su bi dokar hana fita da aka saka a wasu jihohi a fadin kasar tare da kauce wa fakewa da zanga-zangar wajen tayar da zaune tsaye.