✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun sasanta da tsohon mijina —Rahma Indimi

Bayan shafe kimanin shekaru 14 ba sa tare, surukar tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, Rahma Indimi ta tabbatar da sassantawa da tsohon mijinta. Rahma…

Bayan shafe kimanin shekaru 14 ba sa tare, surukar tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, Rahma Indimi ta tabbatar da sassantawa da tsohon mijinta.

Rahma ta tabbatar da sasantawa da Muhammad Ibrahim Babangida ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram (@rahma_yi) ranar Talata.

Sakon nata na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara tsegumi kan alakarta da tsohon mijin nata.

Rahma dai diya ce ga hamshakin attajirin nan na jihar Borno, Muhammad Indimi.

Rahaman ta ce a yanzu sun fahimci juna ita dan tsohon mijin nata kuma suna cikin kwanciyar hankali.

To sai dai wasu makusantan ma’auratan sun ce sasantawar ba wai tana nufin sun koma zaman aure ba ne; kawai dai yanzu abubuwa sun soma daidaita ne kuma ana gaisawa, sabanin da can da ba sa ga maciji.

A shekarun baya dai Rahman ta zargi tsohon mijin nata da kokarin rabata da ‘ya’yan da suka haifa tare wadanda tun da ma suke wajenta, inda ta sha alwashin cigaba da rike su.