✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun sha kama fitattun ’yan siyasa masu ta’ammali da miyagun kwayoyi —Marwa

Hadin kan da Buhari ya ba mu, da kuma jajircewar kananan ma’aikata ya kai mu ga wannan nasara.

Shugaban Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA Janar Buba Marwa, ya ce sun sha kama wasu fitattun ’yan siyasa masu wannan mummunar dabi’a.

Buba Marwa ya fadi haka ne a lokacin da yake bayyana shirin Majalisar Dokokin Najeriya na amincewa da dokar yi wa ’yan siyasa gwajin miyagun kwayoyi gabanin tsayawa takara ko kuma rike duk wani ofishi.

Cikin tattaunawarsa da BBC Buba Marwa ya ce suna wannan yunkurin ne saboda sun sha kama fitattun ’yan siyasa da ke ta’ammali da irin wadannan miyagun kwayoyi, wanda kuma hakan ba abu ba ne mai kyau.

­Yanzu bai zama doka ba amma a nan gaba zai zama doka, saboda kwamitinmu na Majalisar Dokokin Najeriya ya mika shawarar neman hakan a hukumance, kuma da sannu za a yi.

“Ba mu ne muka fara bullo da wannan doka ba, tun tuni Jihar Kano ta fara yin gwajin kwaya ga duk wani mai rike da mukami a gwamnatance, kuma za a fadada irin wannan mataki a fadin kasar baki daya,” in ji Marwa.

Ta’ammali da miyagun kwayoyi na daya daga cikin manyan abubuwan da Najeriya ke fuskanta na koma baya a ’yan shekarun nan.

Wani abu da Buba Marwa ya ce sun samu damar dakile wa cikin shekaru biyu da ya kwashe yana gudanar da aikinsa a matsayin shugaban NDLEA.

“Mun kama tan na miyagun kwayoyi kusan tan 5,700 wanda da sun isa inda aka nufa da su cikin wannan kasa da an samu gagarumar matsala.

“Sai kana da kayan shaye-shayen za ka iya shan abin da kake so, mun dakile shigowar wadannan kayayyaki wani abu da muke alfahari da shi.

Buba Marwa ya ce cikin aikin hukumar NDLEA akwai taimaka wa masu ta’ammali da kwayoyin wadanda shaye-shayen ya zamar musu jiki, domin mayar da su cikin hayyacinsu.

“Akwai asibitotin da muke da su wadanda nan muke kai su domin su samu kulawa ta musamman, kuma sama da mutum dubu goma sha tara 19,000 aka yi wa wannan aiki.

­“Mun kama masu sayar da wadannan kwayoyi sama da dubu uku inda aka gurfanar da su gaban shari’a karshe aka aike da su gidan yari.

­“Manyan diloli sama da 34 mun cafke su, wanda hakan ya matukar rage yadda kwayoyi ke yawo a Najeriya,” in ji Buba.

Shugaban NDLEA din ya kara da cewa hadin kan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su, da kuma jajircewar da kananan ma’aikatan da ke kaman suka yi ne ya kai su ga wannan nasara.