✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shawo kan matsalolin da muka fuskanta a zaben Shugaban Kasa – INEC

INEC ta kuma ce ranar Talata za ta kammala dora sakamakon zaben Shugaban Kasa a shafinta

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta gyara dukkan matsalolin da ta fuskanta a yayin zaben Shugaban Kasa da na ’Yan Majalisun Tarayya gabanin zaben Gwamnonin da za a yi a karshen makon nan.

Kwamishinan Hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Ya ce INEC ta koyi muhimman darussa, kuma za ta yi amfani da su wajen gyara matsalolin da za a iya fuskanta a zaben na Gwamnoni.

Festus ya kuma ce sun yi iya bakin kokarinsu wajen tabbatar da an magance matsalar sashen duba sakamakon zabe na shafin hukumar, wanda aka fi sani da IReV.

Ya ce yanzu haka sashen yada labaran hukumar ya yi shirin ko ta kwana, ko da za a fuskanci kalubale yayin dora sakamakon zabe daga rumfunan zabe a shafin.

Ko a makon da ya gabata, sai da Kotun Daukaka Kara ta amince wa hukumar INEC da ta sake sabunta bayanan da ke kan na’urar tantance masu zabe ta BVAS gabanin zaben na karshen mako.

Sai dai daga bisani INEC ta sanar da dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon 11 ga wata don samun damar sabunta bayanan.

A wani labarin kuma, Kwamishinan ya ce sama da rumfunan zabe 170,000 ne aka dora sakamakon zaben Shugaban Kasarsu da na Majalisar Tarayya a shafin na INEC.

Ya kuma ce sake sabunta bayanan BVAS din zai kammala ranar Talatar nan, a wani bangare na ci gaba da shirye-shiryen zaben.